Addu'a Ga Wanda Bashi Yai Masa Yawa |
Addu'ar da Annabi Isa AS yake koyawa sahabbansa. yace da daya daga cikin ku yanada bashi na zinari kwatankwacin girman dutsen Uhud, idan ya lazumci karanta ta Allah zai hore masa abinda zai biya bashin dashi
Idan bashi yayi maka yawa ka rasa yadda zakayi, sai ka ware lokaci ka yawaita karanta wannan addu'ar. An samo ta daga cikin Sahihul Hakam juz'i na 1: hadisi na 515. hadisin Aishatu RA inda tace: "Wata rana babana ya shigo wajena. wato Abubakar Saddiq RA. sai yace 'Aisha ko kinji addu'ar da Annabi SAW ya fada?' sai nace waccece? sai yace:
"Addu'ar da Annabi Isa AS yake koyawa sahabbansa. yace da daya daga cikin ku yanada bashi na zinari kwatankwacin girman dutsen Uhud, idan ya lazumci karanta ta Allah zai hore masa abinda zai biya bashin dashi". Ga addu'ar kamar haka:
" اللهم فارج الهم اللهم كاشف الغم مجيب الدعوة المضطرين رحمان
الدنيا والآخرة ورحيمهما أنت ترحمني فارحمني رَحْمَة تُغنني بها عن
رحمة من سواك ".
"Allahumma farijil hammi, allahumma kashiful gammi mujibud da'awatil mubdarina, rahmanid dunya wal akhiratii warahimaha, anta tarhamni farhamni rahmatan tagnini biha an rahmatan man siwak".
Addu'ar Bashi Ta Biyu 2
In mutum zai lazimci karanta wannan addu'ar koda bashin da ake binsa yakai girman dutsen uhudu na zinari Allah zai hore masa abinda zai biya da yardarsa.
Turmizi ya ruwaito daga Aliyu Ibn Abi Talib. Yace: "Ya Aliyu an sa mani fansa domin in fanshi kaina sai Aliyu yace masa: "Zan sanar dakai addu'a wacce Manzon Allah SAW ya sanar dani, cewa in kanada bashin da ake binka koda yakai girman dutse in kana karanta ta Allah zai biya maka" Ga addu'ar kamar haka:
" اللهم اكفني بحلالك عن حرامك واغنني بفضلك عمن سواك ".
"Allahumma akfini bi halalika an haramika wa agnini bi fadlika an man siwak".
(Hadisin Turmizi juz'i na 5: hadisi na 3523).