Addu'a Don Samun Saukin Al'amura

Addu'a Don Samun Saukin Al'amura
Addu'a Don Samun Saukin Al'amura



Mutumin da al'amura sukayi masa tsanani, rayuwa tayi masa wuya kuma ya shiga cikin tashin hankali. Kai ko dama macece mai juna biyu ta shiga cikin tsoro da firgici, koda takai ace za'a yimata aikine wato CS, ta gigice hankalinta ya tashi. In har zata rinka karanta wannan addu'ar Insha Allah komai zai zo mata cikin sauki da yardar Allah.


Ibn Hajar ya ruwaito daga Hassan Ibn Ahmad Ibn Said yace; Babarsa tanada juna biyu sai ta shiga damuwa, kuma macece mai tsoron Allah da taqawa. Wata rana ta kwanta bacci sai ta roki Allah daya kawo mata sauki tattare da cikin da take dauke dashi, kuma ta sauka lafiya sannan Allah SWT ya yaye mata duk abinda ke damunta. Ta kwanta bacci sai tayi mafarkin Annabi SAW yace; "Ya Ummu Habib, karanta wannan addu'ar;


"يَا مُسَيَّرَ الشَّدِيدَ وَيَا مُلِيَنِ الْحَدِيدَ وَيَا مُنْجِزَ الْوَعِيدَ وَيَامَنْ هُوَ كُلَّ يَوْمٍ فِي أَمْرٍ جَدِيدٍ أَخْرِجْنِي مِنْ خِلْقِ الْمَضِيقِ إِلَى أَوْسَعِ الطَّرِيقِ بِكَ أَدْفَعُ مَالَا أَطِيقُ وَلَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ الْعَلِيَّ الْعَظِيمِ"


"Ya musairul shadid, wa ya mulinul hadid, wa ya munjizul wa'id, wa ya man huwa kulli yaumin fi amrin jadid, akhrijni min khalqil madiq ila awsa'id dariqi bika adfa'u mala adeequ wala haula wala quwwata illa billahil aliyul azeem".


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post