Addu'a Don Samun Kariya Daga Sharrin Makiya

Addu'a Don Samun Kariya Daga Sharrin Makiya
Addu'a Don Samun Kariya Daga Sharrin Makiya 


Ana son duk lokacin da kika yi sallah cikin sallolin farilla guda biyar. kinyi azkar, kar ki tashi daga inda kike sai kin karanta wannan addu'ar kamar haka. 


Da yawa daga cikin mutane basu san suna da makiya ba, dan ko wani gani yake yadda zuciyarsa take tas haka takowa take babu hassada ko bakin ciki. To abin ba haka yake ba. Wani ko riga yaga ka canza haushin ka yake ji bare yaga ka fito kana fara'a sai 'yaji kamar ya kashe kansa saboda bakin ciki da haushin ka da yakeji. Kai baka ma sani ba.


Wata kuma abokiyar zamantace da taji miji yana yawan yabonta don kyautata masa da takeyi sai ta nemi ta sabautata ko ta haukatar da ita, ko kuma ta fitar da ita daga gidan. Wata kuma dangin mijin ne zasu tasa ta gaba, da zarar sunga tana zaune lafiya da mijinta sai su nemi su kaita gurin 'yan tsubbu ko 'yan bori dan a sabautata.


Wata ma uwar mijin ne da kanta zata taso ta gaba. ta kaita wurin bokaye dan ta lalata zaman lafiyar ta da mijin. To koma dai menene, ga addu'ar da ya kamata ki lazimci karantawa. Allah SWT zai baki kariya daga dukkan sharrin mutum ko aljani, sai dai aga sunata kulla miki sharri amma ko ajikinki. Suyi ta kashe dukiyarsu wurin bokaye ke kuma ko sisi baki kashe ba amma kin fisu kwanciyar hankali.


Don haka ana son duk lokacin da kika yi sallah cikin sallolin farilla guda biyar. kinyi azkar, kar ki tashi daga inda kike sai kin karanta wannan addu'ar kamar haka. 

سورَةُ الرُّومِ آية 19-17


Suratur Rum ayata 17-19. Zaki karanta shj kafa bakwai sannan sai ki kara da;


"فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُلْ حَسْبِيَ اللَّهِ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ العظيم"

Suratut Taubah ayar karshe.


In kinsan sunan me yi miki hassadar sai ki kira sunanta ko sunanshi ki nemi Allah SWT yayi miki kariya daga sharrinsu, Idan kuma baki sani ba sai ki nemi tsarin Allah daga dukkan mahassada. Da yardar Allah duk makirci da tsafe-tsafe ko sihiri ba zai yi tasiri a kanki ba.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post