Addu'a Dan Warkar Da Ciwon Da Aka Rasa Gane Kanshi

Addu'a Dan Warkar Da Ciwon Da Aka Rasa Gane Kanshi
Addu'a Dan Warkar Da Ciwon Da Aka Rasa Gane Kanshi 


Imam Malik ya taba samun wani ciwo da yaje aikin hajji a makkah, ciwon da har ya hanashi bacci. Yace beyi wani magani ba da ya wuce wannan addu'ar 


Imam Bukhari da Abu Dawud da Nisa'i da Ibn Majah sun ruwaito daga Abdullahi Ibn Abbas RA. Yace wata rana muna tareda manzon Allah SAW, sai mukaji wata kara a sama, sai Manzon Allah yake gaya mun," Abdullahi Ibn Abbas kasan karar menene?" sai nace Allah da Manzonsa suka sani, sai yace," Wata kofa ce aka bude ta a sama, ba'a taba budeta ba sai yau, wasu mala'iku suka zo, basu taba zuwa duniya ba sai yau, sukayi mun albishir da wani haske guda biyu, wanda ba'a taba bawa wani annabi irin wannan hasken guda biyu ba sai yau".


Sai nace; "Ya Rasulullahi wannan wani haske ne?", sai yace:"Suratul Fatiha da Amanar Rasulu". Annabi yace babu wani abu da 'dan Adam zai roki Allah dasu in har ya karanta su face Allah ya bashi. Koda wani ciwo ne da mutum, anyi maganinsa an rasa gane ciwon, in har zai rinka samun zamzam mai kyau ko ruwan sama ko ruwan rijiya da safe, kafin ya fito harkokinsa, ya karanta Fatiha da Amanar Rasulu ya tofa ya sha. Kowane irin ciwo ne Allah zai raba shi dashi da yardarsa.


Imam Malik ya taba samun wani ciwo da yaje aikin hajji a makkah, ciwon da har ya hanashi bacci. Yace beyi wani magani ba da ya wuce wannan. Zamzam yake diba ya karanta Fatiha da Amanar Rasulu ya tofa ya sha ya shafe jikinsa. Ita yayi har ya warke.


A Kore Bokaye Da 'Yan Tsubbu 

Munsani mafi yawan bokaye da 'yan tsubbu mata ne customominsu. Kama daga maganin mallaka, ko maganin jinnu ko kuma maganin farin jini. So muke a rufe wannan shafin gaba daya. Mu dauki bangare na daya wanda nasan ko damfarar mutane da akeyi dasu aka fi fakewa a cuce su.


Munsan aljanu gaskiya ne kuma babu me inkaharinsu, kama daga Jinnul Ashiq, Jinnul Tabdil, Amirul jinnu, Jinnu Aswad, da makamantansu.


Anan yakamata mu kawo muku guraren da jinnu suka fi zama a gidajenku da jikinku. Sannan mu koya muku matakan da zaku bi don rabuwa dasu kwata-kwata. Da kuma matakan da zaku bi dan kar su dawo jikinku.


Guraren Da Aljanu Suka Fi Zama 

Farko akwai gurare guda goma 10 da bai kamata iyayenmu mata suyi wasa dasu ba. Saboda guri ne matattaran aljanu. Gasu kamar haka;


1. kofar daki

2. Saman daki cikin ceiling

3. Dakin daya dade a kulle

4. Bandaki. Shiyasa Annabi SAW ya koyar damu addu'ar da in zamu shiga bandaki mu karanta ta. Ga addu'ar kamar haka;


"اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ الْخُبُثِ وَالْخَبَائِثِ"


"Allahumma inni a'uzubika minal khubthi wal khaba'ith". Sannan mu shiga da kafar hagu, in zamu fito mu karanta:


"بِسْمِ اللَّهِ غُفْرَانَكَ"


"Bismillahi Gufranak". Sannan mu fito da kafar dama dan gujema gamo da aljanu.


5. Gurin da ake yawan hura wuta, misali kitchen. Shiyasa in kika doshi kitchen ana so ki karantal Suratul Fatiha da ayatul kursiyyu dan neman tsari daga shedan da kuma aljanu.


6. Shinfidar da aka yita ba'a kwanta akai ba har tsawon lokaci. Annabi SAW yace shinfida kala hudu ce; shinfidar maigida, da shinfidar uwargida, da shinfidar bakinku, ta hudun itace shinfidar aljanu in baku kwanta ba tom zasu zo su kwanta akai. Shiyasa akace in zaku kwanta kan shimfida ku karkade gefenta sau uku da bismillah.


7. Sai kuma hotuna, ko kuma zanen da akayi aka aje a daki ko parlor. Aljanu suna maida hoton gurin hutawarsu.


8. Kayan da aka ratayesu suka dau lokaci ba'a saka ba. ba'a kuma ninke ba ko da kuwa suna wardrobe ne aljanu suna zama cikinsu.


9. Gurin wanke-wanke. Shiyasa aka hanamu zubar da ruwan zafi a gurin wanke-wanke.


10. Sai kuma gindin bola ko rijiya. Shiyasa aka hanamu tara bola a gida ba gaira babu dalili. Haka idan ma muna da rijiya a gidanmu mu rinka kulle ta idan dare yayi.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post