Abunda Kesa Mace Yin Feshin Ruwan Ni'ima

Abunda Kesa Mace Yin Feshin Ruwan Ni'ima
Abunda Kesa Mace Yin Feshin Ruwan Ni'ima 


Masana na kimiya a likitance dai sun kasa gano hakikanin abunda yake jawo mace yin feshi. Sai dai binciken da suka gudanar, kaso 45 zuwa 50 cikin 100 na mata ne kadai suke yin wannan feshin.


A baya mun yi bayanin ma'anan feshi da kuma babbancin ruwan feshi dana fitsari. Abu na gaba da yakamata kuma mu nemi sani shine abunda ke jawo mace tayi shi wannan feshin.


Masana na kimiya a likitance dai sun kasa gano hakikanin abunda yake jawo mace yin feshi. Sai dai binciken da suka gudanar, kaso 45 zuwa 50 cikin 100 na mata ne kadai suke yin wannan feshin. Masanan suka ce matan da suke da Skene's glands a farjinsu sune suke yin wannan feshin.


Shi dai Skene's glands wani kulutu ne dan kararrami da ba a iya ganinsu da ido guda biyu a kowani bangare na mafitsaran mace dake taimaka mata wajen fidda ruwa a lokacin da ta kamu da sha'awa na Jima'i. Mata masu wannan Skene's glands sune suke yin feshi saboda yadda halitar ke tunkudowa mace ruwan sha'awa idan Jima'i zata yi. Haka nan idan fitsari zata yi nan ma ya sa fitsarin fita cikin sauri da kuma sauki. Wannan halitar ba duk mata suke da shi ba, maza ne suke da shi wanda wani lokacin yake rikedewa ya girma ya zama gwaiwa.


Sai dai kuma ba duk mata suke feshi iri daya ba. Wasu matan suna yinsa da yawa, wasu kuma bai da yawa amma dai suna iya jika shinfidarsu. Akwai matan da duk bayan dakika 10 zasu iya fesowa, wasu kuwa idan sunyi sau daya sai sun kara daukan lokaci sannan suyi, wasu kuwa da sun siyaya shi basa sake yi sai kuma a wani Jima'in.

 

Wasu matan feshin na zuwa musu da zafi, wasu kuwa cikin sauki suke fesowa abunsu. Mata da yawa sun shiga rudani da tashin hankali a farkon soma yin feshi, dayawa da basu da illimi akansa suna zaton sun kamune da wata cuta. Don haka sai su garzaya wajen likita domin neman agaji, anan ne ake musu bayanin baiwar dake garesu. Masu rashin sa'a kuma idan suka je wajen masu bada maganin da basu da illimin abun, kara firgitasu suke, suyi ta cin Kudinsu da sunan sun kamu da cuta. Sam feshi bai da alaka da wata cuta sai ma tabbatar wa mai yi tanada cikenken lafiya.


Tunda munji bayanin abunda ke sa mace yin feshi daga jikinta. To ta yaya ake zungoro abun har kuma ta feso shi. Amsar na darasi na gaba.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post