Abubuwan Dake Karya Azumi Da Wanda Basa Karya Azumi

Abubuwan Dake Karya Azumi Da Wanda Basa Karya Azumi 

Abubuwan Dake Karya Azumi Da Abubuwan Da Basa Karya Azumi 


Za ku kawo muku abubuwan dake karya azumi da kuma abubuwan da basa karya azumi, domin akwai wasu da sun kasa bambance abinda ke karya musu azumi da kuma wanda basa karya azumi. 


Watan Ramadan wata ne maigirma ga musulmai wanda suke yin azumi daga fitowar ranar zuwa faduwar ta a kullum har tsawon kwanaki 29 zuwa 30. Azumi na nufin kuracewa daga ci ko shan wani abu kamar ruwa tsawon yini. Azumi na daga shikashikan musulunci 5 kuma hanya ce da musulmi ke kara kusanta kansa ga Allah S.W.T. 


Akwai abubuwan dake karya azumi, ma'ana yin wasu abubuwa a lokacin da ake yin azumi suna iya lalata azumin mutum wanda kuma daga baya sai ya yi ramuwa.


abubuwan dake karya azumi

Daga cikin abubuwan dake karya azumi ga su kamar yadda Allah S.W.T ya fada a cikin Alkur’ani maigirma. 


1) Ci ko shan duk wani abu; Mutum yaci abinci ko kuma ya sha wani abu wanda zai wuce maƙoshin sa alhalin yana sane da yin hakan, wannan yana ɓata azumi

2) Shan Kayan Maye; Shaye-shayen kayan maye kamar taba sigari, giya, sholi da dukkan wasu kayan gusar da hankali na karya azumi. 

3) Jima'i(saduwa); Mutum ya sadu da matansa ko mace ta sadu da mijinta wannan yana daga cikin abubuwan dake karya azumi

4) Istimna'i (masturbation);  Mutum yayi amfani da wani abu domin ya biyawa kansa ɓuƙata har sha'awansa ta tashi ya fitar da farin ruwa wannan shima yana bata azumi

5) Alfasha; Mutum yayi ma Allah ƙarya ko Annabawan Allah ko Iyalan gidan Manzon Allah wannan shima yan ɓata azumi

6) Shakar iska ko kura; Idan Mutum ya bari ƙura ya shige har cikin maƙoshin sa wannan shima yana ɓata azumi

7) Janaba; Mutum yasan yanada janaba yaƙiyin wanka kuma a watan azumi har asubahi tayi wannan shima yana karya azumi

8) Amai; Mutum ya ƙirƙiri amai a lokacin da yake azumi shima wannan yana daga cikin abubuwan dake karya azumi

9) Shan Magani; idan ana azumi ba'a shan magani idan kuwa har mutum ya sha magani lokacin azumi tabbas azumin ya karye sai dai daga baya ya rama. 

10) Jinin Ala'da; idan mace tana yin jinin al'ada ko na biki babu azumi a kanta sai dai daga baya ta rama. Sannan kuma yin allura ko daukar jini duk yana daga cikin abunda ke karya azumi 


Wannan sune abubuwan dake karya azumi, bari kuma mu kawo muku wasu daga cikin abubuwan da basa karya azumi. 


Abubuwan Da Basa Karya Azumi

Akwai wasu abubuwa da dama wanda yinsu ba zai karya azumi ba, domin akwai wadanda ke tunanin yin wannan abubuwan zai iya jawo musu karyewar azumin su. Ga abubuwan kamar haka;


1) Cin Abinci Da Mantuwa, idan mai azumi ya ci ko shan wani abu cikin Mantuwa azumin sa yana nan. 

2) Saduwa Da Mace Dalilin Mantuwa; idan mai azumi ya sadu da matarsa lokacin yana azumi cikin Mantuwa azumin sa bai karye ba. 

3) Wanke Baki; mutane da dama suna kokonto kan wannan, domin wasu na cewa idan ana azumi ba'a wanke baki har sai lokacin da aka kai azumin. Amma wannan ba haka bane, mai azumi yana iya wanke bakinsa da kowane abu yake so idan har abin bai koma cikinsa ba 

4) Shafa Turare; yin amfani da turare ko mai da dukkan wani nau'in kayan kamshi baya bata azumi. Jin Kamshin Turare Na Ruwa Ko Na Hayaki

5) Fitar Jini; fitar da jini kamar yin habo, ko fashewar baki ko jin rauni baya karya azumi. 

6) Yin Allura Ta Jijiya Ko ta Nama Ko ta Masu ciwon Sugar baya cikin abinda ke karya azumi 

7) Yin mafarkin saduwa; idan mutum yai mafarki yana Jima'i azumin sa bai karye ba domin ba da sanin sa hakan ya faru ba. Wanda Yayi Mafarki Yana Axumi Har Ya Fidda Maniyyi, Sai Yayi Wanka Amma Axuminsa Yana nan.

8)  shaka ruwa; zuba ruwa a baki ba tare da an hadiye ba baya daga cikin abinda me karya azumi. Sannan Hadiye Yawu Ko Majina shima baya karya azumi. 

9) Bayar Da Gudun Mawa Na Jini, idan mutum ya bayar da jini a lokacin da yake azumi baya karya azumi. 

10) Jin Rauni Ko Ciwo; idan mutum yai rauni a Jikinsa hakan baya nufin azumin sa ya karye. Sannan yin kwalliya ko tozali basa karya azumi 


Wadannan sune abubuwan da basa karya azumi, ina fatan kun ilimantu daga abubuwan da kuka Karanta. Sannan Insha Allah zamuci gaba daga inda muka Tsaya anan gaba, Allah subhanahu wata'ala yayi mana gudummuwa alfarman Annabin Rahama da Iyalan gidansa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post