Jinin budurci |
Maza Ku Sani Cewa Rashin Ganin Jinin Budurci Ba Shine Ke Nunawa Mace Ba Budurwa ce Ba
Korafın samari ko ince angwaye yayi yawa kan cewa 'yan matan da suke aura ba sune suka fara kwanciya dasu ba suna zuwa ba tare da budurcin su ba. Hujjar su anan ita ce, sunyi saduwar Aure ta farko da matan nasu amma basu ga jini ya fito ba.
Ku Sani cewa ganin jinin budurci a ranar farko da miji ya fara saduwa da matarsa ba hujja bace da za'a yi wa mace kallon 'yar Iska ba. Akwai abubuwa da dama dake haddasa rashin ganin jini ga budurwa a saduwar farko.
BUDURCI:- shi dai budurci Wata fata ce dake cikin farjin mace matashiya, kuma fatar ba mai kwari bace sannan tana iya yagewa da zarar ta samu takura. Kuma wannan takura dake sa fatar ta yage abubuwa da yawa ke jawo shi.
Dalilin Da Zai Sa Ango Rashin Ganin Jinin Budurci
Mace tana rasa budurcinta ne ta wadannan hanyoyin kamar haka;
1. Saduwa da namiji
2. Daukar kaya mai nauyi
3. Guje-guje
4. Hawan keke
5. Hawan doki ko jaki
6. Mummunar faduwa
7. Sanya dan yatsa a farji
8. Haihuwa da sauransu
Wasu matan ko an sadu dasu fatar budurcinsu bata yagewa har sai sun zo wajen haihuwa ananne zata yage.
Dan haka nake kira ga samari dake shirin yin aure don Allah duk wanda ya auri mace Budurwa kar yace lallai sai ya ga wannan jinin budurci, Idan har baka ga wannan jinin ba to kar ka yiwa matarka kallon 'yar iska ko mazinaciya domin inda yar iska ce ko mazinaciya da kasani tun kafın kuyi Auren.
Tunda lokacin da kayi bincike kafin kayi Auren, domin ba'a zama da zargi don da zarar Zargi Ya fara shiga Aure To aure zai lalace. Allah ya kiyaye mu da kiyayewarsa Kuma Allah yasa 'yan uwana maza su Fahimta, Allah ya bamu Yaya na gari tare da Zuriya daiyiba Ameen.