Abubuwan 3 Da Mata Ke Fara Duba Ga Namiji Kafin Su Karbi Soyayyarsa |
Mata suna fara duba 3 ga namiji kafin su karbi soyayyarsa
Maza da dama na tsoron tunkarar macen da suka gani suke so a Karon farko. Koda ma ta tsaya ta saurare shi, akwai wasu abubuwa da take fara duba kafin ta amince da namijin. Don haka ne ba'a son namiji kai tsaye ya tunkari mace ba tare da kinsti ba. Akwai wasu abubuwa 3 da kusan duk mace Ke fara duba ga namjin da ya je wajenta, gasu kamar haka;
Abubuwan 3 Da Mata Ke Fara Duba Ga Namiji Kafin Su Karbi Soyayyarsa
1. Fuska; Babban abinda mace ke fara kalla ga namijin da ya tunkareta shine fuskarsa, abinda take tunani mai kyau ne, fari ne, baki ne mai dogon hanci ne da sauran su. Idan bakai daidai da zabin ranta ba zakaga babu wani karsashi tare da ita. Shiyasa ake so idan ka kusanci mace idan kuka hada ido kasance mai kwarin gwiwar zaka samu karbuwa wajenta. Kuma ka kasance kana kallon ta idan kana magana da ita, hakan zai sa ko baka yi daidai da zabin da take so ba ka iya samun kyakkyawar amsa daga gareta
2. Tsawo; Abu na biyu da mace ke duba ga saurayin da ya tunkare ta shine ya girman sa yake gajere ne ko kuma dogo ne, munsan cewa mata basa son gajeren namiji. Musamman gajerun mata na son samun dogon namiji. Kowane yanayi kake kai dai ka yadda da kanka kuma ka saka karfin gwiwar zaka samu nasara.
3. Ado; Kafin Ka tunkari mace ka tabbatar da cewa shigar da kayi mai daukar hankali ce, kasa kaya masu kyau na ado, wanda idan mace ta Kalle ka za ta san lallai kai din 'dan-gayu' ne hakan zai sa tai saurin tsayawa ta saurare ka. Ka tabbatar kaji kwarin gwiwa a ranka yayin tunkarar mace sai dai ina baka shawara Kada ka yi abinda yafi karfin ka misali siyan sutura da tafi karfin ka ko aro kayan da ba naka ba. Duk irin munin ka idan kana yin shiga mai kyau Zaka samu karbuwa wajen mace.
Wadannan sune abubuwa 3 da mata ke fara duba ga namiji kafin su aminta dashi. Nasan kun koyi abubuwa da dama bayan kammala wannan rubutun, wane karin bayani za ku yi kan wadannan abubuwan 3 na tunkarar mace? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku a sashin sharhi.