Abubuwa 3 dake jawo yawan fitsari |
Dalilai da yawa kamar tsufa, juna biyu, cutuka kamar siga kumburin mafitsara da sauran abubuwa da dama na iya jawo yawan yin fitsari akai-akai
Yawan tashi fitsari musamman cikin dare wani al'amari ne dake damun wasu mutane da dama a yanzu musamman lokacin yanayin sanyi da muke ciki. A Likitance ana kiran hakan da nocturia kuma wannan yanayin yana shafar maza da mata.
Dalilai da yawa kamar tsufa, juna biyu, cutuka kamar siga kumburin mafitsara da sauran abubuwa da dama na iya jawo yawan yin fitsari akai-akai cikin dare.
Duk da haka, baya ga wadannan dalilai da muka bayyana akwai wasu dabi'u gama gari da muke aiwatarwa yau da kullum, wanda kan haddasa mana yawan yin fitsari. A wannan topic zan kawo muku 3 daga cikin abubuwan da za ku daina yi don gujewa yawan fitsari akai-akai.
Abubuwa 3 Da Za Ku Daina Yi Idan Kuna Son Daina Yawan Fitsari Musamman Cikin Dare
1. Iyakance Shan Abubuwa; musamman shan ruwa awanni biyu kafin kwanciya bacci zai taimaka wajen rage adadin ruwa a koda. A cewar binciken healthline koda na taka rawa wajen gudanar da motsin ruwa a jiki wanda ke adanawa a mafitsara dake sa saurin fitsari. Shan ruwa mai yawa kafin kwanciyar bacci yana sa mafitsara ta cika mutum yai ta zaryar zuwa fitsari cikin dare. Don haka ana bada shawarar rage shan ruwa da yawa karfin kwanciya.
2. Wani abu kuma da za mu daina yi da dare shine shan giya da sauran kayan sha na maye. Wadannan abubuwan na taimakawa wajen kara yawan ruwa a mafitsara dake sa yawaitar yin fitsari. Rage shan giya da kayan maye zai taimaka muku wajen rage yin fitsari cikin dare akai-akai.
3. Na karshe, ana bada shawarar rage shan abubuwan dake dauke da sugar kafin kwanciya. Shan abubuwan dake dauke da zaki na taimakawa wajen kara yawan yin fitsari wanda ke hana mutum samun bacci yadda ya kamata. Ana bada shawarar rage ci ko shan abubuwan dake dauke da zaki kafin kwanciya bacci.
Barin yin wadannan abubuwan 3 kafin kwanciya bacci ta hanyar rage shan giya ko shan abubuwan dake dauke da zaki da yawan shan ruwa na taimaka muku yawan tashi yin fitsari cikin dare.