Abubuwa 10 Da Mata Ke Yi Da Maza Ke Birgesu

Abubuwa 10 Da Mata Ke Yi Da Maza Ke Jindadi
Abubuwa 10 Da Mata Ke Yi Da Maza Ke Birgesu 


Abubuwan Da Mata Ke Yi Wanda Ke Birge Maza Batare Da Matan Sun San Yana Saka Mazan Su Ji Dadi Ba


Ko namiji na ya fara yin soyayya da mace ko kuma yana cikin yin soyayya da ita akwai wasu abubuwan daukar hankali da mata ke yi wanda ke birge maza. Kuma suna yin wadannan abubuwan ne ba tare da tunanin maza na so ba. 


Kodayake yana da wuya a bayyana abubuwan da maza suke so, duk da haka akwai wasu abubuwan da matan ke yi wanda maza ke so basically tare da sun nuna suna so ba amma yana birge su. 


Akwai wasu abubuwa da mata za su yi tunanin ba ya birge maza wanda ya hadar da dabi'u da wasu ayyuka da suke yi na yau da kullum, amma shin wannan wane abubuwan ne? 


Ga wasu Abubuwa 10 Da Mata Ke Yi Da Maza Ke So

1. Kwanatar Da Kanki A Kan Kirjinsa; Mace ta kwantar da kanta a kirjin mijinta a yayin da suke zaune suna kallon TV shi kuma ya dora hannunsa a Jikinta musamman bayan ta yi ayyukan gida ta gaji hakan yana birge namiji 

2. Neman Agaji (support); namiji na jindadin mace ta nuna masa shi mataimaki ne a wajenta, ta nuna zai iya tallafa mata a kowane yanayi, hakan yana sa namiji yaji dadi

3. Tura Masa Sako(text); abubuwan da mata ke yi da maza ke so, ki fara tura masa sako, maza na son a nuna musu so, ko da baya tunaninki idan kina tura masa sako zai fara tunanin ki, sannan hakan zai sa ya dinga jin nishadi ganin kina tunawa dashi ko bai ganki ko jin muryarki ba. 

4. Wanke Masa Kaya; Wannan na daga cikin abubuwan dake kara birge mace wajen mijinta ba tare da ya nuna mata ba. Amma da yawa daga cikin mata basa iya yin hakan. 

5. Ki Bashi Mamaki Da Abinda Yakeso; Abinda Mike ganin karami ne amma ya wuce hakan, musamman ki yi masa doughnut, meatpie da sauransu. 

6. Ki Tuna Masa Yadda Kike Kaunarsa; nuna so ga wanda ake so ba abune mai sauki ba sai an jajirce, akwai dabaru da hanyoyin da ake nuna masoyi ana Kaunarsa, kamar yi masa kiss yayin da zai bar gida da rako shi har waje. 

7. Kiyaye Abubuwan Da Yake So Da Wanda Baya So; macen dake kula da kiyaye abubuwan da mijinta ke so da wanda baya so, misali yi masa irin miyar da yake so ko kuma yi masa wanda baya so, hakan yana saka namiji yaji babu kamarta. 

8. Bayyana Masa Gaskiya Kan Komai; yana daga abubuwan da maza ke so yake kuma birge su kamar bayyana gaskiya daga wajen mace hakan yana birge su. 

9. Kula Da Iyayensa; wannan yana daga cikin abinda ke birge maza idan matansu suna yi amma basu fiya fitowa su bayyanawa matan ba. 

10. Tsafta; Wannan kunsan ba sai an yi wani dogon bayani ba domin kuwa babu abinda ke kara son mace a Zuciyar namiji kamar tsafta, idan ta kasance mai tsafta zai kara sonta a ransa 


Wannan sune abubuwa 10 da mata ke yi jindadi da kara Kaunarsu. Shin kina yiwa mijinki wadannan abubuwan, ko kuma wasu daga ciki kike yi? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku a kasan comment.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post