Abincin Gargajiya Dake Gina Jiki Da Kara Kiba Cikin Sauki

Abincin Gargajiya Dake Gina Jiki Da Kara Kiba Cikin Sauki
Abincin Gargajiya Dake Gina Jiki Da Kara Kiba Cikin Sauki 


Abincin Gargajiya Da Cin Su ke Kara Gina Jiki Da Kara Kiba Cikin Sauki 


Abinci yana daya daga cikin manyan ababen da kusan shi ne farko wajen samarda jini ga gangar jikin Dan- adam. Kenan dai ba a rayuwa matukar babu jini, shi kuma jini baya samuwa a dole sai an ci abinci.


Sai dai yawaitar sarrafa abinci iri iri saboda yanda zamani keta juyawa, wanda shi wannan abincin a mafiyawa kusan kashi 80 daga cikin 100 na mahadinsa (ingredients) nasa kayan maikone da zaki wadanda mun san illarsu ba karamace bace ga lafıyarmu.


A yau shi wannan abincin ya mamaye abincinmu na gargajiya inda kusan yaran dake tasowa a wannan lokacin wannan da zaka tambayesu wani abinci na gargajiya to ba zasu gaya maka shi ba, kuma ba zasu iya cin sa ba, dan zaki da maiko ya canza dandanon harshen nasu.


Mafi yawan rashin lafıyoyin da muke gani daga abincin da muke ta'ammali da shi ne. Shi harshe shi ke son kayan zaki da kayan maiko da sauran ababuwan kwalama. Amma shi ciki baya jin dadin kayan zaki da maiko. Asali wahalda shi su ke yi. Shi kuma jini daga abinci ne, sannan ba kayan maiko da kayan zaki ke samarda jini da lafıya mai inganci a jiki ba.


Abincin mutanen da, baya dauke da kayan maiqo da zaqi da wasu sauran sinadarai kamar na yau, shi yasa kaga mutanen da sun fi na yanzu lafıya da juriya da kuma karfi.


Akwi abincinmu na gargajiya dake da matukar amfanin gaske fiye da na yanzu, yana daukeda sinadirri masu kara yawaitar jini, masu bunkasa karfın garkuwar jiki, masu samar da karfın qassa ga jiki, masu gina jiki, masu sauwaqe kumburin ciki da dai sauransu.


Abincin Gargajiya Dake Gina Jiki Da Kara Kiba Cikin Sauki 


Ga jerin abincin dake gina jiki kamar haka: 


1-Tuwon Dawa; dawa tana samarda karfi sosai ga jikin mutum, tana sa mutum idan ya ci baya jin cikinsa ya kumbure, kuma bata haifar da taurin bayan gari(hard stool). Mai cin tuwon dawa zaiga bayan garinsa da laushi ba ciwo ko wahalar fita.


2. Tuwon masara: dukda yake akwai wadanda suka camfa masara da wai tana shan jini kuma bata da amfani wanda wannan labarine kawai na rashin tushe balle makama. Tuwon Masara na saurin narkewa a cikin kankanin lokaci kuma bata qabe ciki, mai neman yawan cin abinci to ya fake cin tuwon mascara (stimulates appetite) mai kashi kamar na dabbobi shi ma ya rinka cin tuwon masara.


3. Gero: (millet) kusan gero ya kasance abincin da ake iya sarrafawa daban daban kama daga ayi tuwonsa, ayi fura da shi, ayi gumball, ayi kunun sa, ayi masa da shi, ayi garinsa a maida shi dambu, da sauran nau'in abinci. Kuma duka zai bada wata fa'ida dake amfanar jiki. Shi ma dai Carbohydrate ne a don haka sai a ci dan a samarwa jiki da karfı.


4-Alkama: daukacin mutane basu san amfanin alkama ba, wasu ko ganinta basu taba yi ba. Akwai post na musamman akan fa'idodin alkama da zan kawo maku da kuma dinbin maganin da take yi. Ana kunun alkama a sha dan magance cutukkan ciki kamar zafın ciki, kumburin ciki, ciwon ciki, karancin haihuwa ga mata da maza, gushewar ni'ima, rauni ga namiji.


Ka nemi alkama a nika ka bayar a rinka yi maka kununta kana sha, a hakika zaka ji dadi kuma lafıyarka zata inganta.


6. Nono: A yau mutanen sun fi son su sayi yoghurt su sha bisa ga nonon shanun da muka gado tun azal, wata damuwa anan ma shi ne akwai yoghurt dinda kamar garin masarane ake gyarawa a zubowa suga a zo ana sayar muna, yau dai ga yoghurt nan kowace iri gani kake ga tsabar zaki tare da ita.


Amma shi nono idan ka same shi kamar kindirmo to sai ka markade ka sha, zaka ji jikinka da kwakwalwarka dama cikinka da wani sauyi na daban, kuma zaka ga yanda jikinka zai canza.


7.Dussar gero idan an surfe aka cire dussar to idan so samune a dake dussar a maidata kamar gumba sai a jefa kanwar tuwo a dama a sha. A hakika tana gina jiki tana inganta lafıyar jiki, tana kara karfın immunity, tana yashe cutukkan ciki tasauwake wahalar bayan gari. Kuma tana sa kaji kana son cin abinci da jin dandanonsa.


8. Miyar kuka: tana da amfani sosai kuma itaciyar a kasar Hausa tafi yawa amma da dama basa son miyar kuka, to a takaice miyar kuka na maganin basir tana kuma kara basir a. bata haifar da kowace irin illa ga jiki. Kuma tana daga cikin hanyoyin kara kiba,


9. Datu: idan an samu kanzon gero ko na dawa ko na shinkafa ko masara to sai a nemi kuli kuli da zogale a hade waje guda a ci sai an koshi, an ci nutrients. Mu daina cewa a dole sai anci kwai an sha madara da nama da su maltina sannan aka ci kaya masu nutrients wallahi wadannan duka sun fi wadannan kayan da muke gani, domin suna samar da kiba, da gyara jiki. 


10. Sobo: A can baya ana shan sobo amma yanzu su dudu milk, bobo da su nutri milk da five alive sun kwace kasuwa.


A hakika Sobo yafı dukkanin kayan drinks din nan da muke gani amfani akwai bincike na musamman da ya tabbatar da haka. Ana samun shi a kauye da birane. Kusan jiki yana da bukata ga dukkanin abinda ke a cikin sobo.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post