Abincin Dake Kara Girman Azzakari |
An Bayyana Nau'in Abinci 5 Dake Taimakawa Wajen Kara Girman Azzakari
Bukatar kowane namiji a zamantakewar aure shine yaga yanada babbar al'aura, wato yana son yaga yana da katon azzakari. Maza da yawa na tunanin girman azzakari shine kololuwar da zai sa su iya jiyar da matansu dadin da suke bukata. Sai dai hakan ba lallai ya zama gaskiya ba.
Maza da yawa na bukatar ganin Azzakarin su ya kai girman inchi bakwai da rabi (7.5)' Wadanda suke da lalurar kankantar azzakari a kullum suna ganin cewa kwayoyi sune kadai abinda zai iya taimaka musu. abinda basu sani ba shine, akwai hanyoyi da dama na asali da zasu taimaka musu wajen samun irin girman azzakarin da kuke bukata. Wato daga inchi biyar 5 zuwa bakwai da rabi (7.5). Zamu yi duba zuwa abinci kala biyar daka iya kara maka girman azzakarinka ba tare da shan wani magani ba.
Masana sun bayyana nau'in abinci 5 da cinsu ke taimakawa namijin dake son samun girman azzakari, idan kana ci da shan wadannan abinci da zan bayyana muku za ku samu biyan bukata. Ga su kamar haka;
1) Albasa: Bincike ya nuna cewa, albasa tana taimakawa sosai wajen hankada jini zuwa sassan jiki daban daban da kuma cikin zuciya. Sannan cin albasa yana hana jini dankarewa a waje daya, ma'ana tana tsinka jini, wanda hakan yana saka jini kewaya ko ina a jiki cikin sauki. wanda shigar jini cikin azzakari akai akai yana matukar taimakawa wajen kara masa girma. Don haka idan baka cin albasa kuma kana son karin wadatar azzakari daga yau sai ka fara.
2) Ayaba: Hasashen masana ya tabbatar da cewa masu ingantacciyar lafıyar zuciya suna da dama ta kara girman azzakarinsu cikin sauki. Ayaba na dauke da sinadarin potassium wanda ke bada kariya ga cututtuka da suka shafi jijiyoyin jini. sannan tana rage yawan sinadarin sodium dake jikin mutum wanda yana cutar wa a jikin mutum. sannan har ila yau tana inganta zagayawar jini a jikin dan adam.
Ingantacciyar lafıyar zuciya da kuma kyakkyawan yanayi na zagayawar jini a jiki shike taimakawa wajen samar da babban azzakari ga mutum.
3) Alayyaho: Wannan ganye ya samo asali daga yankin tekun fasha halittaccen abinci ne dake kara girman azzakari. Wato yana tattare da sinadarin Magnesium, wanda ke inganta zagayawar jini cikin jijiyoyin azzakari. cin alayyaho akan kari zai bada gudunmawa sosai wajen kara girman azzakari.
4) Kifi: Kamar yadda muka ambata a batun albasa, duk abincin da ke iya taimakawa wajen zagayawar jini a jiki, lallai yana da kyau wajen taimakon kara girman azzakari. wannan kalar kifi na (salmon) dake kunshe da sinadarin omega-3 wanda ke tsinka jini. yana da matukar amfani wajen kara girma da kauri na azzakari.
5) Kankana; kankana na dauke da wani sinadari na citrulline wanda ke kara girman azzakari. lokacin da aka sha kankana tana samar da sinadarin L-arginine wanda ke bada sinadarin nitric oxide, aikinta shine yawan hankada jini cikin azzakari. yawaita shan kankana kan agaza wa mazaje wajen kara girman mazakuta.
Wadannan sune Kalolin abincin dake kara girman azzakari, suna da yawa sosai amma wadannan sune mafi saukin saye da kuma satrafawa. Nan gaba za mu kawo muku karin bayani kan abubuwan dake taimakawa girman azzakari.