Yan bindiga sun kashe shugaban makaranta tare da yin garkuwa da matarsa da Jaririnsu a Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban makaranta, Idris Abu Sufyan tare da yin garkuwa da matarsa da jaririnsa a kauyen Kuriga da ke karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.
Lindaikeji ta tattaro cewa ‘yan bindigan sun kai farmaki gidan Sufyan ne a daren ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, 2024, inda suka harbe shi har lahira kafin su tafi da matarsa da dansa zuwa inda ba a san inda suke ba.
Har zuwa rasuwarsa, Sufyan ya kasance shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) Kuriga.