Yadda Tashin Bom Ya Halaka Mutane 8, Tare Da Jikkata Da Dama A Jihar Borno |
Yadda Tashin Bom Ya Halaka Mutane 8, Tare Da Jikkata Da Dama A Jihar Borno
Rahotanni daga jihar Borno ya tabbatar cewa akalla mutane 8 ne ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wasu bama-bamai a kan hanyar Ngala zuwa Dikwa a Karamar Hukumar Ngala.
Majiyar ta ce fashewar bom din ya yi kaca-kaca da wasu motocin biyu yaddda ba za a iya gyara su ba.
Wata babbar majiya ta jami’an farin kaya na JTF ta ce motocin biyu kirar Isuzu da wata babbar mota ce suka taka bom din kuma ana fargabar kashe kusan dukkan fasinjojin ciki.
“Wadannan motocin dai sun bar garin Ngala da misalin karfe 9 na safe, yayin da lamarin ya faru a nisan kilomita 15,” in ji majiyar.
Aminiya ta ruwaito cewa, tashin bama-baman ya faru ne a tazarar kilomita 15 daga Maiduguri, babban birnin jihar.