Yadda Mace Zata Gamsar Da Mijinta A Kwanciyar Aure |
Matan Aure Gareku: Yadda Mace Zata Gamsar Da Mijinta A Kwanciyar Aure
Gamsar da namiji a jima'ince yafı sauki wajen gamsar da mace, duk kuwa da cewa dukkannin halittan da aka yiwa mace a jima'ince shima namiji yana da irinsa.
Haka kuma kamar yadda ake samun harijin namiji haka nan ma ake samun harijar mace, yadda ake samu mazan da suke jimawa babu gajiya a lokacin jima'i hakama matan. Ana samun maza da mata ragwaye a wajen jima'i da kuma wadanda sam jima'in ma bata damesu ba a dukkanin mace da namiji.
Da akwai wasu mazan da basu cika son doguwar wasannin motsa sha'awa ba, wasu kuwa suna bukatan lokaci mai tsawo ana masu wasa duk kuwa da macen tafı namiji bukatar wasan motsa sha'awa mai tsawo.
Abu na farko da ya kamata mace ta fahimta a tattare da mijinta shine abunda yafı bukata a yayi wasannin motsa sha'awa da kuma lokacin kwanciya irin na jima'i, domin da akwai inda da zaran mace ta tabawa mijinta maimakon ta motsa mishi sha'awarsa sai kawai sha'awar tashi ya gushe.
Hakama a kwanciyar jima'i, yana da kyau ki fahimci irin yanayin kwanciyar da mijinki yake so. Shi yasa malamai na jima'i suke cewa sadarwa a jima'i yanada matukar amfani ga ma'aurata domin ta hanyar ce ake samun gamsuwa.