Yadda Ake Yin Matsi Da Lalle Da Bagaruwa |
Yadda Ake Yin Matsi Da Lalle Da Bagaruwa, Wani bincike ya bayyana cewa ana yin amfani da garin bagaruwa don matsi
Yaya za mu yi amfani da bagaruwa da lalle don yin matsi? Itace tambayar da na samu da yawa daga wajen mata a cikin wannan satin. Hakan yasa na yi bincike domin gano yadda ake yin matsi da lalle da bagaruwa.
Da farko dai ina son na baiwa mata shawara kan sanin abinda ya kamata su dinga yi a lokacin da suka ji labarin ana yin amfani da abu kaza don magance abu kaza, yana da kyau idan kuka ji Irin wannan labarin ku dinga tuntubar masana don baku shawara ko kuma sanar daku yadda ake yi idan ya tabbata ana yi.
matsi da lalle da bagaruwa
Wani bincike ya bayyana cewa ana yin amfani da garin bagaruwa don matsi, bagaruwa na dauke da sinadaran dake taimakawa tsuke farjin mace. Wannan yasa suke tunanin tafasa garin bagaruwa da zama a cikinsa na tsawon lokaci na taimakawa matse gaba, sai dai babu wani tabbacin hakan daga likitoci.
Shima garin lalle ana yinsa ne daga ganyen lalle, shi dai galibi an fi yin amfani dashi don yin kunshi ko gyaran gashi, da canja launin gashi. Babu wani bayani daga wajen likitoci kan ko lalle yana matse gaban mace ko inganta lafiyar farji. Yin amfani da lalle don yin matsi kan iya jawo kaikayi, ciwo.
Don haka iya bincike na babu wata hanya da ake yin matsi da lalle da bagaruwa. Saboda haka ina tunasar daku duk abinda kukaji ance yana matsi kafin ku yi shi yana da kyau ku tuntubi masana don jin shawarari akai, akan zai taimaka muku. Ina fatan wannan bayanan za su gamsar daku musamman wanda ke son yin matsi da lalle da bagaruwa.