matsi da garin lalle, |
Shin zan iya yin amfani da garin lalle don matsi?
Na yi bincike game da tambaya da na samu kan yin matsi da garin lalle, inda na tattaro muku hanyoyi da kuma wasu bayanai a kan tasirin lalle ga lafiyar mace.
Wani bincike ya tabbatar da yin amfani da garin lalle don yin matsi, sai dai ban samu cikakken bayani kan yadda ake yin amfani da garin lalle don yin masti. Hakan yasa na tuntubi wasu masana kiwon lafiya kan sahihancin yin amfani da garin lalle don yin matsi.
Sai dai sun tabbatar min babu wani binciken su da ya gano ana yin amfani da lalle don yin matsi, sun ce shi lalle ana amfani dashi ne don canja launin ko kalar gashi, ko kuma yin ado kamar yadda aka man mata suna yi.
Don haka dai ba'a yin amfani da garin lalle don a yi matsi, kuma shi lalle yana iya haifar da kaikayin fata, ciwon fata ko fesowar kuraje, don haka babu yadda Za'a ce mace ta yi amfani dashi a Farjin ta. Don haka ku kiyaye yin amfani da lalle a gaban ku, yana da kyau ku tuntubi likitoci kafin yin irin wadannan abubuwan.