Yadda Ake Yin Maganin HIV Na Islamic

Yadda Ake Yin Maganin HIV Na Islamic
Maganin HIV Na Islamic


Maganin HIV Na Islamic, Mutane da yawa na fama da wannan cutar cikinsu har da yawa daga cikin yan uwa musulmi


Ina mai matukar baku hakuri idan kana ko kina daya daga cikin wadanda wannan cuta ta HIV ta faru daku. Kanjamau ko HIV cuta ce babba da babu wani dan adam a doron kasa dake fatan ya same ta. Ita wannan cutar babbar barazana ce duba da yadda take lalata garkuwa jiki 


Maganin HIV Na Islamic

Mutane da yawa na fama da wannan cutar cikinsu har da yawa daga cikin yan uwa musulmi, duk da masana kiwon lafiya na duniya har zuwa yanzu basu iya gano maganin cutar HIV kai tsaye ba sai dai maganin dake iya rage radadin ciwon. 


Wannan dalilin ne yasa mutane da yawa musamman musulmi ke neman sanin maganin HIV na islamic, wato yadda za su magance cutar a musulunce. Wannan yasa mukai wani dogon bincike done gano ta yadda Za'a yi maganin cutar a Islamic. 


Har zuwa lokacin hada wannan topic bamu iya gano wani magani kai tsaye da za'a yi amfani dashi don magance cutar kanjamau ba. Amma akwai wasu matakai da mutane za su iya bi don kare kansu daga kamuwa da cutar HIV. 


1) Ku guji yin Jima'i barkatai ba ta hanyar aure ba, domin yin Jima'i barkatai yana jawo barazanar kamuwa da HIV. 


2) Saduwa ta dubura, dama duk musulmi yasan Allah ya hana yin saduwa ta dubura, idan kana son kare kanka daga kamuwa da wannan cutar sai ku nisanci saduwa ta dubura. 


Wannan matakai ne da wadanda basuda cutar za su kiyaye kansu. Amma ga wadanda suke da cutar abinda ya dace su yi shine su dinga tuntubar likitoci don neman shawarwari da kuma karbar magani don kara karfin garkuwan jiki. Amma babu wani maganin HIV na islamic da kai tsaye ke warkar da cutar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post