Kazar maijego |
Yadda Ake Yin Hadin Kazar Maijego Don Mata Masu Aure
Bayan kazar amarya da kuma kazar mallaka, suma mata musamman wadanda suka haihu akwai hadin kazar su wacce ake yi bayan mace ta haihu da kwanaki 40 domin dawo da martabarta wajen mijinta.
Wannan hadin kazar na maijego yana da tasiri sosai wajen kara lafiyar mace, da kara mata dandano da nishadi a wajen mijinta. Idan maijego ta yi hadin wannan kazar za ta dawo kamar sabuwar amarya wajen mijinta.
Hadin Kazar Maijego
Yadda ake yin wannan hadin na kazar maijego za ki nemi wadannan abubuwa kamar haka;
- Budurwar kaza (na gida)
- Saiwar malmo
- Saiwar bagaruwa
- Garin zogale
- Gishirin gallo
- Hakin daka
- Garin biyarana
- Da ruwan kabewa
- Nonon rakumi
Yadda Ake Yin Hadin Kazar Maijego
Idan kin samu dukkan wadannan abubuwan da na lissafa a sama ki gyara kazarki sannan ki cire kayan cikin, ki tabbatar kin daka wadannan sauran abubuwan sai ki zuba su cikin kazar ki dinketa. Sai ki zuba ruwan kabewa cikin tukunya sai ki saka kazar a ciki ki saka gishiri da sauran kayan hadin girki da kike so.
Ki bar kazar ta dafu sosai ta yi romo, sai ki cinye kazarki ke kadai ki lashe romon ba tare da kin baiwa kowa ba. Masana sun ce idan kika ci wannan kazar kika shanye romon har ki kara yin wata haihuwar yana yi miki aiki a jikin ki.
Amma shi wannan hadin kazar maijego ne kadai kuma sai ta yi kwana 40 bayan haihuwa sannan ake yinsa. Da fatan kun amfana sannan da fatan za ku sanarwa da sauran mata.