Yadda Ake Yin Addu'ar Warware Sihiri |
Yadda Ake Yin Addu'ar Warware Sihiri Cikin Yardar Allah Kuma A Samu Nasara
Mutanen da ke da sihiri a jikinsu na neman Mafita, wasu na neman magungunan da za su yi amfani dashi wasu kuwa na neman addu'ar da za su yi domin kawo karshen matsalar. Wannan dalilin yasa naga ya dace na kawo muku yadda za ku warware sihiri da ikon Allah.
Addu'ar Warware Sihiri
Za'a samu ganyen magarya guda bakwai (7) a daddakasu da dutse ko wani abu sai a zuba cikin ruwa, sannan a kara baki kusa da ruwan ta yadda numfashin karatun zai dinga sauka cikin ruwan, sai a karanta wadannan ayoyin kamar haka:
I. Ayatul Kursiyyi
II. Sura til A'araf daga aya ta 117 zuwa ta 122
III. Suratu Yunus daga aya ta 79 zuwa 82
IV. Suratu D.H. daga aya ta 65 zuwa 70
V. Suratul Kafirun
VI. Suratul Ikhlas
VII. Suratul Falaq
VIII. Suratun Nas.
Bayan an kammala karatun sai a sha ruwan sau uku (3) (lokutta daban-daban koda bayan mintuna ne) sannan ayi wanka da sauran a wuri mai tsarki.
Haka kuma wadannan Addu'o'i suna da amfani ga mijin da aka hana kusantar iyalinsa da kuma wadda duk lokacin da aka tsayar da maganar aure sai ta watse/lalace ba tare da wani dalili ba. Allah kayi muna kariya daga sharrin halittunka ma'abuta sharri.