Yadda Ake Warware Sihiri Cikin Sauki Da Yardar Allah |
Matakan Yadda Ake Warware Sihiri Cikin Sauki Da Yardar Allah
Warware sihiri ba abune mai sauki ba musamman ga wadanda basu san yadda akeso yi ba, hakan yasa yau na kawo muku hanyoyin yadda za ku yi don ku warware sihiri cikin ikon Allah.
Yadda Ake Warware Sihiri Cikin Sauki Da Yardar Allah
A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai 7, idan an samu busassu sunfı, sai a nika ko a daka su dawo gari, sai a zuba cikin ruwan nan me tsafta. Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yin numfashi yana shiga cikin ruwan, hucin karatun ya wadatar ba sai an tofa ba.
Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara). A karanta Suratul A'araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.
Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82. Suratul Kafirun (Qulya) kafa daya 1 Falaki da Nasi kafa uku- uku.
Sai a karanta wannan addu'a Allahumma rabban-nas az'hibil ba'as ashfi waantash-shafi la shifa'a illa shifa'uk shifa'un la yugadiru sakama kafa uku 3 Sannan za'a iya karawa da wannan addu'a
"Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika kafa uku 3"
Insha Allahu ta'ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu 2 a rana safe da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, banda bayangida (toilet) ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan da sati guda kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi.
Sannan kuma mai fama da cutar da ba a san kanta ba ma zai iya amfani da wannan dama domin neman waraka a gun Allah. Haka cututtukan zamanin nan da aka kasa gano magungunan su za a iya amfani da wannan hanya don neman waraka a gun Allah.
Ba sai mutum yaje wajen boka an danfare shi ba, basai an yi maka/ miki sihiri ba, mutum zai iya yi domin tsima jikin sa (rigakafi) don kariya daga sharrin masharranta a gun Allahu SWT.
Don Allah duk wanda ya yi amfani da wannan fatawah kuma ya sami waraka ya yi kokari ya yiwa Annabi salati 3 a matsayin abin sadaqah. Idan kuma bai samu damar yi ba babu komi insha a Allah.