Yadda Ake Gane Siffofin Mace Mai Aji - Android Pols

Yadda Ake Gane Siffofin Mace Mai Aji 


Mace mai aji itace a koda yaushe take suturta jikinta domin tana matukar kishin kanta.


Idan ka samu mace mai aji kayi dacen samun mata dukda suna da yawa wuyar sha'ani kafin ka iya sace zuciyar su. A yau mun kawo muku wasu daga cikin siffofin mace mai aji. 


Yadda Ake Gane Siffofin Mace Mai Aji 

Itace macen da tasan darajar kanta da kuma addinita ta hanyar gujewa duk abinda zai taba mutum cinta.

Itace macen da bata shiga abinda babu ruwanta domin gudun kada arainata. 

Mace mai aji itace a koda yaushe take suturta jikinta domin tana matukar kishin kanta.

Itace wadda bata tara samari ko kuma kawaye barkatai sabod gujema kana nan maganganu  ko kuma a wulakanta ta.

Mace mai aji itace macen da bata daukan raini don ba ta raina kowa itama bataso a rainata.

Mace mai aji, itace waddda bakajin hayaniyar ta a inda ake yawaita surutu don tafi kowa kishin muryanta.

Itace macen da bata saka hotunanta a social media saboda tana matukar tsoron abinda zai saka a ga surarta. 

Mace mai aji, Itace mace mai girmama duk wadda ya girma ma mata don tasan darajar su koda akwai wadanda basa sonta.

Itace komin sanda takema namiji bata bari har yaga fuskar da zaiyi wasa da sasan jikinta. Domin ita mace mai aji tana kishin Jikinta. 

Mace mai aji kana iya samun soyayyarta  amma ba cikin sauki bane zata iya bari ka  shawo kanta, domin suna da aji sosai. 

Mace mai aji takam koma mara aji a lokacin da take matukar sonka hakan na faruwane saboda tunaninta kaine zaka aureta.

Itace mace mai qualityn da kowani namiji yake mafarkin ganin ya aureta. Domin kuwa duk abinda ake nema suna dashi. 

Banbancin ne tsakanin jan aji da kuma girman kai da mace keyi ammah saika sa hankali  gami da tsaida tunnaninka waje daya sanan ka nazarta.

Yar uwa ki kasance mace mai aji koda kuwa mutane za su yi ta sukarki da bakaken magan ganu akanki hakan shawarace kyauta.

Wadannan sune wasu daga cikin siffofin mace mai aji, wanda duk wani namiji yake buri da kaunar samu. Sai dai a yanzu mata masu aji suna da wuyar samu sosai. Kuma duk inda kaga mace mai aji za kaga ta bambanta da sauran mata. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post