Yadda Ake Gane Jarababben Namiji
![]() |
Yadda Ake Gane Jarababben Namiji |
Masana Sun Bayyana Wasu Alamomin Yadda Ake Gane Jarababben Namiji
Shin kunsan yadda ake iya gane jarababben namiji daga kallon sa? Nasan wasu da yawa za su shiga rudani kan wannan tambayar, amma babu mamaki kuma nasan idan kuka Karanta za ku karu.
Jarababben namiji wasu na kiransa da hariji saboda baya gajiya da jima’i, koda yaushe cikin bukatar kasancewa da mace yake. Shiyasa da wuya ka samu jarababben namiji wanda yake iya rayuwa da mace 1.
Wasu na kallon maza masu irin wannan siffar a matsayin larura, amma dai bincike ya tabbatar da cewa ba cuta bane kawai yanayin halitta ne na dan Adam. Don haka duk wanda yake da wannan siffar Kada ya dauka cewa cuta ne.
Idan mace ta auri miji mai irin wannan siffar idan kuma ita ba mai irinta bace tana shan wuya a wasu lokuta ma har akai ga rabuwa saboda rashin samun daidaito a tsakani. Dama tsakanin mace da namiji duk wanda yafi wani bukatar sha'awa ana iya samun matsala a zamantakewar aure.
yadda ake gane jarababben namiji
Duk wanda yake jarababbe a wajen sha'awa tsakanin mace ko namiji sun san kansu, idan ma basu sani ba ga wasu alamomi da zan bayyana muku wanda Indai kuna yinsu yana nuna kai jarababben namiji ne. Ga alamomin kamar haka;
Jarabar son jimai, shi jarababben namiji ko kallon mace yai sha'awarsa motsawa take har idonsa ya canja kala. Nan da nan zai ji sha'awar yana son saduwa da ita.
Yawan Sha'awa mai karfi, shi yana da karfin sha'awa sosai, don baya iya zama haka kawai, shiyasa jarababben maza anfi samun su da laifin yin fyade, domin har kananan yara suna iya haike musu.
Aikata wasa da Al'aura(istimna'i) Zaka same su kullum suna dabiar aikata istimna'i koda kuwa suna da mata domin mace daya bata iya gamsar da jarababben namiji. Shiyasa idan suna da hali suke kara aure basa iya zama da mace 1 ko 2.
Kallon fina-finan batsa, shifa namiji mai irin wannan siffar baya gajiya da kallon fina-finan nuna tsiraici domin shi sai ya kalla zai ji a rasa kamar dashi ake yi, shiyasa basa bari a karbi wayarsu don gudun Kada aga abubuwan dake ciki da suke kalla.
Wannan Sune alamomin yadda ake gane jarababben namiji, shin bayan Karanta wannan topic zuwa yanzu ka gano matsayinka? Kai jarababben ne ko kuma akasin hakan, ku bayyana mana ra'ayoyin ku a sashin comment.
Leave Comments
Post a Comment