Yadda Ake Gane Alamomin Shafar Aljanu

Yadda Ake Gane Alamomin Shafar Aljanu

 Alamomin Shafar Aljanu 


Idan Kaji Daya Daga Cikin Wadannan Alamomin Yana Nuna Alamomin Shafar Aljanu 


Mutane da yawa na yin tambya shin akwai wasu alamomi da ake iya gane shafar aljanu? Eh, yadda zaka gane cewa Aljanu sun shafeka, ko kuma sun shafi waninka.


Ganin yadda wannan tambaya ta yi yawa yasa na yanke shawarar kawo muku bayanai da kuma hanyoyin yadda za ku gane alamomin shafar aljanu. Wadannan alamomin sun kasu zuwa gida biyu. Akwai na fili, akwai kuma wadanda basu faruwa sai a lokacin barci.


Alamomin Shafar Aljani Na 'Boye 

1. Bushewar idanu: Zaka ga mutum ya kwanta akan shimfıdarsa amma barcin ba zai zo masa ba, sai can tsakiyar dare ko kuma wajen Asubah.


2. Yawan farkawa daga barci A FIRGICE!. Yana daga cikin alamun shafar aljanu mutum ya dinga firgita a lokacin barci, Wani zaka ga kusan duk minti talatin sai ya farka, ko kasa da haka.


3. Dannau: Mutum yana kwance zai ji wani BAKIN ALJANI yazo ya danneshi. Zai yi ta IHU!. Amma babu mai jinsa. Wani lokacin wasu sunfi yinsa da safe bayan sallar asubah.


4. Mafarkai Masu Firgitarwa: Kamar kayi mafarkin an biyoka za'a yanka ka, ko kuma mafarkin fadowa daga wani tsauni, ko kuma kaga hallaka karara, idan ka farka zaka ji jikinka duk yana zufa.


5. Mafarkin Namun Daji: Ganin miyagun dabbobi a mafarki kamar macizai, Karnuka, Kyanwa, Rakumi mai fada, Damusa, Saniya, Bera, suna bin mutum zasu kamashi, da sauran alamu makamancinsu.


6. Tauna A Cikin Barci. (kaji mutum yana barci amma yana taune-taune). Amma kai ne kawai za kaji kana tauna kamar kana cin abinci. 


7. Dariya ko Kuka, ko Ihu A Cikin Barci, wasu idan suna barci sai aji suna yin dariya ko kuma ihu, kai daga jin hakan kasan babu lafiya. 


8. Kaga mutum yana barci amma ya tashi tsaye yayi tafiya, sannan ya dawo ya kwanta alhali ko farkawa bai yi ba. Shi bai san ma hakan ya faru dashi ba. 


9. Mafarkin afkawa cikin ruwa, ko Jini, ko wani mummunan rami. Shima wanna alamomin shafar aljanu ne da zaka gane. 


10. Mafarkin Matattu, ko ganinka a MAKABARTA, ko wajen yanka dabbobi, ko kwata, ko Juji, ko tsakiyar Daji mai duhu. Suma alamomin shafar aljani ne. 


11. Mafarkin Gajerun Mutane, ko dogaye tsala-tsala. Ko farare Sol, ko bakake WULUK, masu ban-tsoro.


12. Mace ta rika yin Mafarkin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita, bisa siffar Mijinta, ko saurayinta, ko mahaifinta, ko dan uwanta, yawancin irin wannan matan suna shan wahala domin shafar da Aljanu sukai musu.


13. Namiji ya rika mafarkin wadansu mata suna zuwa masa suna kwanciya dashi. Shima alamomin boye ne na shafar aljani. 


Alamomin Shafar Aljanu Na Fili 

Mun kammala yin bayani kan alamomin bayyana ko shafar aljani na boye, yanzu Kuma za mu yi bayani kan alamun zahiri. 


1. CIWON ΚΑΙ : Marar jin magani. Ko an sha magani ba zai dena ba. Kuma gobe ko jibi ma sai ya dawo.


2) FADUWAR GABA: Kaji kirjinka yana bugawa  (kamar zai fashe). Kuma haka kawai ba tare da wani labarin tashin hankali ba. 


3) Shagala daga daina bin Allah ko duk wani abinda ya shafi addini kamar Zikirin Allah, karatun Alqur'ani, da sauran abinda Allah yake so, kai kuma sai kaji baka so. 


4) BAKIN CIKI: Haka kawai babu wani dalili sai kaji ranka yana ta baci, kana jin haushin kowa da kowa ba tare da wani dalili ba.


5) RIKICEWAR TUNANI: Kaji kamar komai ya cabe maka, Ka rasa yadda zakayi kaji babu abinda yake yi maka dadi. 


6) Rashin lafıyar wata gaba ko jiki. Amma likitocin zamani sun gama bincike sun kasa ganowa ko magance cutar. Wannan alamomin shafar aljanu ne na zahiri da ake samun mutane da ita. 


7) Rikicewar Jinin haila. Rashin zuwansa akan lokaci ko kuma zuwansa fiye da kima.


8. Yawan zubewar Juna-biyu. Ko kuma rashin samunsa kwata-kwata. Mata da dama suna fuskantar wannan matsalar. 


9. Jin tafıyar kiyashi ajikinka ko yaushe. Sai kaji kamar wani abin na yi maka yawo a jiki amma da zarar ka taba bazaka ji komai ba. 


10. Jin maganganu masu tsoratarwa ba tare da kaga mai maganar ba. Sai kaji kamar ana yi maka magana amma kuma bazaka ga kowa ba. 


11. Jin tsananin sha'awar aikata sabon Allah. Kaji kamar ana ingizaka. Lokuta da dama za kaji kana son ka sabawa Allah, amma kuma idan kayi sai kayi nadama. 


12. Yawan mantuwar karatu, ko rashin fahimtarsa. Wato toshewar basira, alhali da can ba haka kake ba. Alamomin shafar aljanu ne. 


13. Yawan jin waswasi ko kokonto ayayin tsarki ko alwala ko Sallah. Lokuta da dama idan mutum ya yi wani abun sai yai ta kokonto. 


14. Yawan Kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba. Mutum kawai sai a ga shi kadai yana dariya ko kuka ba tare da wani dalili ba kai kasan wannan aikin aljani ne. 


15. Jin Kasala mai tsanani tare da nauyin jiki. Koda yaushe kaji baka son yin wani aiki kai ta jin kasala da ciwon jiki. 


16. Tsoron shiga cikin jama'a, ka rika jin kamar zasu hallaka ka, alhali kuma ba haka bane.


17. Idan kina tafiya ki rika jin kamar wani yana binki a baya. Alamomi shafar aljanu ne 


18. Yawan kiyayyar juna a tsakanin ma'aurata. Idan mijinki baya nan kiji kina mutukar sonsa. Amma da zarar ya dawo sai ki rika ganinsa kamar dodo, ki rika jin baki son ganinsa ko jin maganarsa.


19. Ciwon ciki ko baya, ko kafa duk alokaci guda kaji kamar ciwon yana yi maka yawo ajikinka. Kuma ko anyi scanning ba za'a ga komai ba.


20. Kaikayin farji, ko Kuraje, ko fitar farin ruwa. Amma ko an sha magani ba ya denawa. Alamar shafar aljanu ne 


21. Jin zafı alokacin saduwa, ko daukewar Ni'ima, bushewar gaba, mace ko namiji za su ji basa jin wata sha'awa. 


22. Son zama a cikin BANDAKI, ko agaban dustbin, ko Juji (bola) ko kuma wani wajen kazanta. 


23. Yawaitar samun matsaloli wajen tsayar da Mijin aure. Da zarar wannan yazo, idan magana ta fara karfı shikenan ba zai dawo ba. Akwai wacce zaka ga ta haura shekaru Talatin aduniya, amma duk da haka Zuciyarta batta son yin auren, ko kuma Ana ta shirya maganar aurenta amma abun ba ya yiwuwa.


Idan kana/Kina fama da alamomi guda biyu ko uku ko sama da haka, kuma kana/Kina bukatar taimako, sai ku yi gaggawar daukar mataki tare da tuntubar Malamai don daukar matakin da ya wuce. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post