Yadda ake family planning na hana daukar ciki |
Yadda ake family planning na hana daukar ciki da ma'aurata za su yi amfani da su
Bisa ga tambayoyi da suka yi yawa kan hanyoyin tsara iyali na hana daukar ciki, a yau za mu duba wannan mas'ala, domin ba kowa ba ne ya yarda a al'adarmu da addininmu cewa tsara iyali na da kyau ko ba shi da shi ba, amma dai domin amfanin masu karatu, da ilmin likitanci akwai lokutan da tsarin ke da amfani matuka da gaske.
Da yake matan yanzu ba irin na da ba ne saboda kujuba-kujubar rayuwa, yawanci matan sun fi son samun doguwar tazara kafın wata haihuwar. Wasu kuma cewa suke matan na yanzu ragwaye ne.
Tsarin family planning na hana daukar ciki
Akwai hanyoyin ba da tazarar haihuwa da dama. Duk kusan sun fi shafar uwargida.
1) Hanyoyin da suka shafi uwar gida yawanci na asibiti ne, kamar allurai da kwayoyi da saka sinadarai daban-daban a mahaifa. Kuma dukkansu suna da 'yan matsaloli wadanda suka hada da rikicewar al'ada ko ciwon mara ko kiba da dai sauran ire-irensu. Wadannan 'yan matsaloli sun bambanta daga wata mace zuwa wata. Wata ciwon mara kawai za ta yi, wata kuma kiba kawai za ta yi, da kuma abin da aka yi amfanin da shi.
Abin da kawai akan ba mata shawara shi ne sai sun gwada kusan kowane kafın su san wanda ya fı karbar su. Hanya ta biyu ta rashin daukar ciki da ta shafi mace ita ce ta shayarwa. Mafı yawan mata (ba duka ba), ba su yin al'ada tsawon shayarwa, ko da kuwa tsawon shekara biyu suka shayar.
To a irin wannan yanayi ba su ba daukar ciki sai sun yaye. Wannan dabara ba ta da wata matsala.
2) Sai kuma kirgen wata. A kirgen wata mai gida zai kaurace wa ranakun hana daukar ciki. Wadannan ranaku su ne kwanakin tsakiyar watan matar, ba watanmu na lissafi ba.
Wannan kirge yana da 'yar rikitarwa, domin sai mace ta tabbatar da cewa watan ta ba ya rikici. Sa'annan kuma yawancin magidanta ma ba su san mene ne kwanakin al'ada ba.
A irin wannan yanayi, dole maigida ya tambayi matarsa ta fahimtar da shi. Ga dan misalin kirgen wata: A mace mai kwanan wata 28, daga rana ta 9 zuwa goma sha 19 su ne ranakun tsakiyar wata wato ranakun da ake kyautata zaton daukar ciki. A mai kwana 32, ranakun 11 zuwa 21 su ne ranakun kyautata zaton daukar ciki.
A mafı yawan lokuta shi ma dai wannan bayani maigida da uwargida sai sun je asibiti ga likitansu ko ungozomar da aka ba horo don fadakar dasu lokuta na hana daukar ciki, an ji karin shawara sa'annan bayanin ke fitowa dalla-dalla.