Yadda ake dafa tantabara amarya

Yadda ake dafa tantabara amarya
Yadda ake dafa tantabara amarya


Yadda ake dafa tantabara amarya domin morewar mata a zamantakewar aurensu 


Shi wannan wani hadine na musamman da ake hada shi ta hanyar tantabara, mun saka masa wannan lakabine sabida irin yanda tantabara take da rike alkawari shima wannan hadin haka yake. Shi wannan naman tantabara yana da amfani ga amarya da uwargida, sanin kowane shi naman tantabara yana da dadi yana da tarihi mai muhimmanci sosai.


 Yanda yake mai dadi idan kika hada daidai kema haka zaki zama, sannan kuma yasa jikinki yayi kyau, sannan kuma zaki samu sinadarai masu yawan gaske zaki samu ni'ima a tare dake kodayaushe.


Yadda ake dafa tantabara amarya

Yanda ake yin wannan hadin na tantabara shine, za ku samu wadannan abubuwa kamar haka;


Tantabara mata da miji (aure)

'Ya'yan ridi(kantu)cokali uku(3)

'Ya'yan habba cokali daya(1)

Garin raihan cokali hudu(4)

'Ya'yan zogale daidai kima


Sai a zuba kayan hadin a tunkunya a dafa su guri daya bayan sun dahu sai a tace su, dama kinriga kin gyara tantabarunki kin wankesu tsaf, saiki zuba wadannan tantabari a tukunya sai ki kawo wannan tataccen ruwan hadin sai ki zuba akai, saiki kawo kayan yaji da dandano ki zuba akai ki rufe, sai sun dahu sosai sai a sauke a ringa ci, kuma yana jimawa sosai yana aiki a jikin mace. 


Wannan hadin na tantabara yana taimakawa sosai wajen inganta dadin zaman aure game ma'aurata, idan mace tana yinsa akai-akai babu shakka za ta kara samun shiga wajen mijinta domin kuwa zai ji babu kamarta. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post