Yadda ake dafa tantabara amarya |
Yadda ake dafa tantabara amarya na musamman domin Sabbin amare
Wani nau'i na hadin tantabara uwar alkawali, dan munyi bayani baya, ga wani kuma kalar daban.
Wannan yana da anfani sosai ga matan aure da amarai. Idan ana so a yi wannan hadin a samu wadannan abubuwan kamar haka;
tantabara guda 2 mace da namiji, a gyarasu, kafın a dafa su, za'a tanidi wannan abubuwan.
a sami cokali 2 na habba da cokali 3 na ridi da garin raihan cokali2, da 'ya yan zogale dai-dai kima.
Yadda ake dafa tantabara amarya
Za'a hada su wuri 1 a dafasu aman banda tantabarun wadannan kayan da na ambata, in sun dafu, sai a sauke a tace ruwan.
Sai a sake daura tataccen ruwan saman wuta sai akawo gyararun tantabarun a zuba ciki adafasu su dafu asa kayan kanshi da abinda ake bukata ciki. Mace ta cinye ita kadai Kada ta sanwa mijinta.