Yadda Ake Dafa Kazar Amarya |
Don Ma'aurata: Yadda Ake Dafa Kazar Amarya |
A matsayin ki na amarya wacce aka yi aurenta ko kuma wacce ake shirin aurenta, shin kinsan yadda ake dafa Kaza ta amarci? Idan baki sani ba yi kokarin Karanta wannan rubutu har zuwa karshe domin zai amfane ki.
Kazar amarya tana da muhimmanci ga duk wata mace musamman wacce take shirin yin aure ko kuma wacce ta yi auren a matsayin amarya. Idan za ku dafa kazar amarya za ku nemi Kayan hadi kamar haka;
Kaza
Kayan miya
Nonon rakumi
Garin ridi
Maggi/gishiri
Citta
Mai
Zuma
Ruwa
Yadda ake girka kazar amarya
A samu kaza wacce bata tsufa ba, son samu ki duba budurwar kaza wadda bata fara kwai ba, a yankata a kwashe duk kayan dake cikinta. Sannan a dan dafata a cikin ruwa, amma kar ta dafu sosai, sai a cire ta.
Sannan ki soya kayan miyarki tare da mai da kuma citta, idan ya soyu sai ki zuba maggi/gishiri da kuma ruwa kadan a ciki.
Sai ki zuba nonon rakumi, garin ridi da kuma zummuwa a ciki ki rufeta ta dafu. Idan ta dahu anaso ki cinyeta ke kadai batare da kin rage wani abu ba. Kuma Kada ki baiwa mijinki idan sabuwar amarya ce ke, idan kuma kina shirin auren ne Kada ki baiwa kowa a gida ke kadai za ki ci.
Bayan kin gama girka kazar, anaso kisamu; garin ridi ki hadashi da madara kokuma madarar rakumi ki motse ki rika sha.