Yadda Aka Kashe Mai Unguwa Sannan Aka Yi Wa Mai Gadi Yankan Rago A Katsina |
Yadda Aka Kashe Mai Unguwa Sannan Aka Yi Wa Mai Gadi Yankan Rago A Katsina
’Yan bindiga sun kashe mai unguwa da dansa da wasu mutun 8 a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.
A daren Laraba ne ’yan bindigar suka yi wa mutanen kisan gilla, ciki har wani mai gadi da suka yi wa yankan rago.
Zugar ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 10 na dare, inda “suka kashe mai unguwa Magaji Haruna da dansa Idris, tare da wasu mutane 3 a gidansa, cewar wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa
“Sun kuma shiga wani kamfani mai suna Tinna Tech inda suka yi wa wani mai gadi yankan rago, dayan kuma suka harbe shi har lahira, sannan suka cinna wa manyan motoci biyu da wata karama wuta.”
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun yi awon gaba da mata dama, amma ba a kai ga tantance adadinsu ba. Tun da misalin karfe 5 na yammacin ranar aka fara fargabar yiwuwar kawo hari, sakamakon ganin ’yan ta’adda a kusa da kauyukna Taka-Tsaba da Yargeza cewar shaidan.
“Duk da cewa jami’an tsaro sun ba mu tabbacin cewa akwai karin jami’ai da za su turo idan har akwai barazanar hari, amma haka ’yan bindigar suka zo suka shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka, jami’an tsaro ba su zo ba.
“Sai da ’yan bindigar suka gama barnarsu suka tafi sannan wata motar jami’an tsaro kwaya daya ta zo,” in ji shi.
Aminiya ta rawaito cewa, mazauna yankunan dai na zargin gaggan jagororin ’yan ta’adda Dankarami da Dangote ne ke aiwatar da hare-haren da ake fama da su a Karamar Hukumar Jibia da kewaye.