Zainab Labarina |
Takaitaccen Tarihin Nana Fidausai Yahaya Wacce Akafi Sani Da Zainab Labarina
Fitacciyar jaruma a shiri mai dogon zango na Labarina Nana Fiddausi wacce akafi sani da Zainab Labarina ta bayyana takaitaccen tarihinta a wata hira da aka yi da ita a shafin BBC Hausa.
Zainab Labarina |
Zainab Labarina 'yar garin Sokoto ce amma asalin ta yar kasar Nijar ce, tana zaune da iyayenta a jihar Sokoto, kuma anan ta yi primary da secondary school duk a jihar Sokoto.
A tattaunawarta da aka yi da ita a shafin BBC Hausa Zainab Labarina ta bayyana cewa ita tun tana karama tana sha'awar yin actin wanda hakan ya ja hankalin ta har ta shigo masana'antar Kannywood.
Nana Fiddausi |
Ta bayyana cewa dan uwanta shine yai mata hanya zuwa ga darakta Ali Nuhu Da kuma Aminu Saira. Sannan kuma iyayenta sun bata goyon baya wanda hakan ya bata karfin gwiwar shiga finafinan Kannywood.
Ta bayyana shirin Labarina mai dogon Zango shine film din ta na farko a masana'antar Kannywood.
Zainab Labarina |
Zainab Labarina ta bayyana cewa role din da ta yi a shirin Labarina ya birgeta sosai, domin kuwa hakan ya jawo mata farin jini da daukaka sosai wajen Masoya.
Sauyin rayuwa da halin matsin tattalin arziki shine babban abinda yake batamin rai ya sakani kuka, Inji Zainab Labarina.
Ta bayyana jarumi Sadiq Sani Sadiq, Maryam Yahaya, Aliyu Tsamiya, daga cikin taurarun jaruman Kannywood da suke kayatar da ita. Sannan ta bayyana wake da shinkafa a matsayin abincin da tafi so.
Zainab Labarina |