Siffofin Samari Mayaudaran Maza |
Siffofin Samari Mayaudaran Maza: Mata sun fi kamuwa da kaunar maza mayaudara fiye da masu son aurensu
Wannan darasin na 'yan mata ne masu soyayya da samari, ina fatan za ku Karanta wannan darasin kuma ku yi amfani da abinda kuka Karanta domin zai amfanar daku.
Yar uwa kisani samari mayaudara sunfi samari na kirki shiga rai, sun fisu iya nuna so da kauna a gareki. Sukan kwantar da kai a gareki komai wulakanci, gasu da naci tun kina kin kula su har sai sunjawo hankalinki.
Hakan yasa gane saurayi mayaudari abune mai wuya domin abune dake zuciya sai dai Idan kinbi wasu matakai zaki iya gane cewa shin wannan saurayin da kike matukar so da kauna a zuciyarki aurenki zai yi ko kuwa mayaudari ne.
Dabarun Da Samari Mayaudara Suke Amfani Dasu Don Yaudarar Yan Mata
- Sukan yi taget din budurwar da suke so su yaudara kodai dan kyanta, ko halittarta ko kimarta ko wani dalili nasu kodan fasikanci.
- Sukanyi nazari akan halayenta kamar akidarta me tafiso wato idan ita ustaziya ce sukan yi shigar ustazai su zo gunta idan sunga dama sukan ruko littafi na ustazai su zo gunki kamar salasa usulu, kitabul tauhid.
Idan ke sayyadace sukan yi miki shigar ya sayyadi su zo miki hira idan sunga dama sai su ruko diwani ko wani dan littafin na kasida, idan ke me yawan karatun soyayyace sai su zo miki da littafan soyayya sabbin shigowa ko cigaban wani littafi shahararre, yana rike a hanunsu.
Idanke ma abociyar son holewace haka zai zo miki da shiga ta yan holewa.
Idan ke abar tausayi ce zaizo da sunan zai taimakeki har makaranta ma zai saki. Zaina bin ra ayinki, bai son saba miki ga su da dadin baki sukanyi miki kuka ko su durkusa miki kasa suna baki hakuri sukan fada miki kalaman kwantar da hankali da rantsuwa wadda saurayi na kirki bazai iya fada mikiba.
Wannan siffofin na sama siffa ce ta samari mayaudara, amma sun fi yin amfani dasu wajen kananan yan mata kamar yan shekara 18 zuwa kasa, sakamako yan mata a wannan lokacin suna da nakasu sosai a tunani. A wannan lokacin soyayya kawai suka sani sukan bujirewa kowa akan soyayya koda iyayensune.
Idan samari zasu yaudari manyan yan mata sukan yaudare sune da kudi ko abubuwan duniya sakamakon a wannan lokacin su manyan mata daga shekara 20 zuwa sama su matsalar su mota, kudi da wasu abubuwan more rayuwa da sauransu.
- Abubuwan rayuwa kamar ara mata mota, yi mata karya za'a saya mata mota ko wasu abubuwa har sai ta saki jiki sannan a yaudareta a gudu
- Wasu mayaudaran samari sukan kai kayan tambaya ko kudin neman aure ko sutura zuwa ga iyayen yarinya, amma daga nan basa sake aiko komai sai su yi ta soyayya da budurwa har sai sun yaudareta
- wasu ma yaudaran samarin sukan yaudareki da hadin bakin abokan sa ta hanyar shirayamiki makirci. Kamar saka miki kwaya a lemo da sauransu .
Dalilin Da Yasa Samari Suke Yin Yaudara
- Daukar fansa, wato watace ta yaudare su sai sukasa yin hakuri sai suje su yaudari wata,
- Rashin tsoran Allah na haqiqa.
- Son suyi fasikanci da budurwa.
- Samun budurwar da za ana zuwa fati da sauran guraren holewa da ita.
Yadda Zaki Yi Maganin Mayaudari
- Kada ki taba yadda ki zurfafa a son saurayi ko waye shi, kuma kome yakawo gidan ku.
- ki zama mai yawaita addu'a da neman kariya daga sharrin samari mayaudara.
- kada ki kuskura kiyi yaudara ko kaka.
- Idan saurayi yazo kafin ki amshi soyayyarsa kibashi akalla kwana 2 ko sati1, kafinnan kije kiyi istikhara akan sa, insha Allah idan bana garine ba bazai dawoba Allah zai wargatsa nufinsa akanki.
- ki yawaita shugo da iyayenki dana sa cikin al'amuranku na soyayya.
- kada kawai don yakawo miki kudin aure ki saki jiki dashi.
- Da zarar kinga nanci a tare dashi ki zage damtse Kada ki yi masa da wasa, domin saurayi matashi masifa ne a cikin minti 10 zai zuba miki dafin da zai shafe tarihin rayuwar ki, ya tozarta ki da dangin ki duka, ya kaskantar dake, ya bata tarihin zuriyarki shi kuma ya gudu ya barki.
Don haka yar uwa idan kin fuskanci saurayi mayaudarine to ki yi gaggawar rabuwa dashi ko kuma ki hada shi da yan uwanki su yi miki maganinsa, hakan zai sa ya rabu dake. Kaso 75 na samari mayaudara sunayine dan su lalataki idan ma dan su kwanta dake kodan suna wasa dake.
Allah ka shiryi masu yin yaudara ka tsare mata daga fadawa hannun mayaudaran maza