coca cola na zubar da ciki |
Shin wai ana iya zubar da ciki Idan aka yi amfani da coca cola? Itace tambayar da na samu daga wasu masu bibiyarmu.
Akwai hanyoyi da dama da ake iya yin amfani dasu domin zubar da ciki, kuma mun kawo muku wasu hanyoyi da dama masu inganci wanda masana suka tabbatar da ingancin su.
Shin coca cola na zubar da ciki?
Wadanda suke yin wannan tambayar ina mai baku hakuri kan hakan, domin duk wanda ya sanar daku cewa coca cola na zubar da ciki babu gaskiya a cikin wannan maganar. Domin na tuntubi masana lafiya musamman na bangaren abinda ke zubar da ciki amma babu wata hanya da tai kama da yin amfani da coca cola don zubar da ciki.
Domin wani binciken ma ya gano cewa yin amfani da coca cola ga mata masu ciki na iya yin barazana ga lafiyar su. Ba'a so mai ciki ta yawaita shan coca cola don yana iya hargitsa cikinta da abinda ke cikinta. Ana bada shawara ga mata masu ciki da su rage yawan shan coca cola, kuma yana da muhimmanci kafin ku gudanar da wasu abubuwan ku tuntuɓi likitoci.
Amma Kada wata mace mai ciki ta yi amfani da wata hanya mara inganci don zubar da ciki, kuma babu wani bincike da ya gano cewa coca cola na zubar da ciki. Duk wani hanya da kuke son ku yi amfani da ita don zubar da ciki ku tabbatar kun nemi shawara daga masana kiwon lafiya.