Lokutan Al’ada Da Daukar Ciki Ga Mata |
Jinin Al’ada da daukar ciki abubuwa ne masu matukar muhimmanci ga rayuwar mata. Sai dai kuma a yawancin lokuta
Ma fi yawan ‘yan mata ba su gane lokacin al’adarsu, saboda jin kunyar tambaya idan suka ga wani canji a jikinsu. ‘Yar uwa, a duk lokacin da kika lura da samuwar wani canji a jikinki, abu na farko da za ki yi shi ne ki fara nazarin abin da ya haifar miki da wannan canji.
Mai yiwuwa abu ne da ya shafi koshin lafiyarki, mai yiwuwa kuma abu ne da bashi da matsala wanda aka saba gani a wurin wasu da suka girme ki. Al’ada da daukar ciki abubuwa ne masu matukar muhimmanci ga rayuwar mata. Sai dai kuma a yawancin lokuta, mata musamman a kasarmu ta Hausa sukan rikice wajen iya rabe lokutan al’ada da kuma lokutan daukar ciki. Domin warware wannan rikicin, a karanta rubutun nan har karshe:
Lokacin Al’ada: Lokaci ne da jini ke fitowa ta al’aurarki wanda kike bukatar yin amfani da wani kyalle mai taushi don kada ya bata miki jiki.
Lokacin Da Jinin Ya Dauke: Kwanakin da jini ya dauke zuwa dawowar wani a wata. Misali, idan kika ga jini ran 11 ga Mayu, sai kuma kika sake gani ran 10 ga Yuni, to zai zama lokacin daukewar jininki shi ne kwana 30 watau, daga 11 ga Mayu zuwa 10 ga Yuni.
Ki Lura: Kada ki yi kuskuren cewa, kwana 28 ne kwanakin daukewar jininki, kowace mace na iya samun bambanci tsakaninta da wata na lokacin daukewar jini, wanda yakan kama daga kwana 21 zuwa kwana 35.
Lokacin Daukar Ciki: Wanna shi ne lokacin da mahaifa ta bude, kuma ana iya samun ciki a wannan lokaci cikin sauki. Lokacin kan fara daga mako 1 kafin fara al’ada. Ga hanya ma fi sauki da za ki lissa kwanakin daukar ciki.
1. Ranar da kika fara ganin jini.
2. Ki duba kwanan wata, sai ki kirga kwana 15 har da ranar farko.
3. Ki lura da ranar da kika fara kirgawa.
4. Ki yi wata alama, kwana uku kafin da kuma bayan wancan kwana 15.
6. Idan kika lura za ki ga kin yi alama a kwana
Wannan kwana 7 su ne kwanakin da mahaifarki ta bude, saboda haka su ne kwanakin daukar ciki. Lokaci ne da idan aka sadu da mace kusan akwai tabbacin daukar ciki da kashi 98 daga cikin dari.
7. Ki yi wannan lissafin a kowane wata, idan kika cire wadannan kwanaki sauran kwanakin ba lallai ba ne in an sadu a dauki ciki. Misali,
1. Idan kin fara al’ada 11 ga Oktoban 2020,
2. Kwana 15 bayan fara al’adar zai zama 25 (har da ranar farko) ga watan Oktoban, mako 2 kenan bayan farawa.
3. Kwana 15 zai kama ranar 25 ga Agustan 2020 kenan.
4. Kwana 3 kafin ranar 25 su ne, 22 da 23 da 24.
5. Kwana 3 bayan 25 ga Agustan 2020 su ne, 26 da 27 da 28.
6. Ranar 22 zuwa 28 ga watan watau kwana 7 kenan, su ne kwanakin da mahaifarki za ta bude. Kar ki manta wannan kwana 7 lokaci ne da maniyi ke zama a mahaifar mace.
Ida aka yi saduwa a cikin wadannan kwanaki, nan da nan maniyin ke fara zama wani sashi na halittar dan’adam. Haka kuma idan ana so a haifi mace, sai a yi kwanciyar auren a tsakanin kwana 3 kafin lokacin daukar ciki, watau ranakun 22, 23 da 24.
Idan kuwa namiji ake so mace ta haifa, sai a yi ibadar auren a lokacin daukar ciki ko kuma kwana 3 bayan ranar 25.
Alamomin Da Ke Nuna Kin Samu Ciki
Ko ba ki je wajen likita ba, za ki san cewa a mako 2 da daukar ciki za ki fara jin wadannan alamun:
1. Ciwon kai.
2. Zafin jiki.
3. Kasala da jin bacci.
4. Girman nononki zai karu kamar lokacin da kike al’ada.
5. Za ki kara sha’awa.
6. Za ki ji kwibinki na yawan ciwo.
7. Za ki dinga jin zafin ciki.
8. Saurin jin wari ko dandano ko gani sosai ko cin abinci da yawa.
9. Al’aurarki za ta yi fadi, in kika sa hannunki za ki ga wani fari-farin abu na fitowa.
Idan kika ji ciwon kai na damunki, sai ki koma ki duba lokacin al’adarki.
Ya kamata ki dinga shan maltina ko madara, kada kuma ki yi gaggawar zuwa kemis da zarar kin ji canji a jikinki, saboda za ki iya warwarewa cikin sauki, domin kuwa wani lokaci yawan shan kwayoyi na da hadari ko kuma ki sha fanadol kawai ya isa.