Mijina Ba Zai Yi Jima'i dani ba Sai Dai Ya Dinga Yin Wasa Da Gabansa Har yai inzali, cewar mata a kotu
Wata mata ta roki kotu ta raba aurensu da mijinta saboda rashin bata hadin kai yai Jima'i da ita, tace sai dai tai masa wasa da al’aurar sa har yai rilisin.
Matar mai suna Doris Unekwu babbar yar kasuwa ce dake zaune a birnin Abuja tare da mijinta Matthias ta roki kotun dake zamanta a Jikwoyi a ranar Alhamis da ta taba aurensu.
Doris ta ce mijin ta Mathias yakan killace kansa yayi ta wasa da al’aurar sa har sai yayi Inzali maimakon ya zo gareta su sadu.
Doris ta ce Matthias na yawan cin zarafin ta ta hanyar yi mata dukan tsiya da zaginta a duk lokacin da ta bata masa rai.
“Babu abin da ban yi ba domin jawo hankalin sa amma duk a banza. Wata rana na kama shi yana wasa da al’aurar sa sannan ya bayyana mun cewa yana haka ne domin koyan wani abu da ya gani a yanar gizo.
“Wata rana kiri-kiri Matthias ya ce mun ya gwamnace ya bata lokacin sa yana hira a waje da ya dawo cikin gida domin wajen ya fi masa kwanciyar hankali.
Doris ta ce a dalilin haka ya sa ta hakura da zaman auren Matthias. Shi kuwa Matthias ya musanta duk abin da Doris ta fada a kansa.
Alkalin kotun Thelma Baba ta shawarci ma’auratan da su je su sassanta kansu a gida. Thelma ta ce za a ci gaba da shari’ar ranar 31 ga Janairu.