Meyasa mata suke jure talaucin iyayensu amma basa iya jurewa talaucin saurayi ko miji
Wani mutum ya Koka Kan irin halin da ya samu kansa a dalilin karayar arziki, yanzu ya shiga mawuyacin hali, domin masoyiyarsa abar Kaunarsa ta juya masa baya.
Magidancin yace lokacin da yake da Iko kowa nasa ne abokanai da makota da yan Uwa har da matarsa wacce bata taba nuna masa bacin ranta a kansa ba tun daga farkon haduwarsu har bayan aurensu.
Amma yanzu abubuwan sun canja matata ta daina sona ta daina kulawa dani ta daina bani hakkina na matsayin mijinta tun bayan da yanzu bani da kudi. Ku bani shawara
Shin Meyasa mata suke iya jure talaucin iyayensu amma basa iya jurewa talaucin saurayi ko miji?