Maryam Yahaya |
Maryam Yahaya a wajen yawon buɗe ido a Alƙahira, babban ƙasar Masar
Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Yahaya ta sake wallafa kayatattun hotunanta daga birnin Alƙahira na kasar Masar wanda suka dauki hankalin Mabiyanta a shafin instagram.
Dubban jama'a ne ke ta bayyana ra'ayoyinsu kan jaruma Maryam Yahaya, inda wasu ke yi mata fatan alheri yayinda kuma wasu ke yi mata tofin ala tsine.
Kwanakin baya an ga jarumar ta wallafa hotunan daga birnin London wanda har ta ziyarci babban filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal wanda yaja cece-Kuce.
Ga hotunan Maryam Yahaya daga birnin Alƙahira