Maganin matsi da lalle

Maganin matsi da lalle
Maganin matsi da lalle


 Don Matan Aure:  Yadda Ake Yin Maganin matsi da lalle

Bincike ya gano cewa lalle na daya daga cikin ganye da ake yin magunguna dashi don matse gaban mace. Bincike ya gano cewa ana yin amfani da ruwan lalle idan aka zuba a cikin baho aka zauna na tsawon wani lokaci yana gyara gaban mace. 


Sun ce yin hakan na taimakawa wajen matse tsokokin farji, sannan yana taimakawa wajen gudanar jini da wanke dukkan dattin dake cikin gaban mace kamar infection. Duk da wannan babu wani tabbacin bayani daga likitoci kan yin matsi da lalle. 


 Yadda Ake Yin Maganin Matsi Da Lalle 

Idan kina son ki yi matsi da lalle ki samu lalle ki tafasa da ruwan zafi sai ki juye a cikin baho ko robar wanka da za ki iya zama a ciki. Idan ruwan ya dan huce yadda ba zai kona miki jiki ba sai ki zauna a ciki na tsawon minti 30 sannan ki zubar da ruwan. 


Haka za ki dinga yi duk bayan kwana 2 har zuwa tsawon wani lokacin, za ki yi mamaki sosai. Domin wannan maganin matsi da lalle an jarraba shi kuma mata da yawa suna yin amfani dashi kuma suna samun nasara. 


Sannan kuma ana yin amfani da man lalle don yin gyaran gashi, wannan hanya ta gyara gashi ta yi fice sosai a kasashen yankin larabawa don gyara gashi. Sai dai ku sani ba'a yin amfani da man lalle don yin matsi don haka sai a kiyaye. 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post