Maganin matsi da alum

Maganin matsi da alum
Maganin matsi da alum


Don Mata, yadda ake yin Maganin matsi da alum


Mata da dama suna tambayata kan yadda ake yin maganin matsi da alum, hakan yasa bayan dogon nazari yau na shirya kawo muku hanyoyin yadda ake yin amfani da alum don yin matsi. 


Shi dai alum na daga cikin abinda aka dade tsawon lokaci ana yin amfani dashi ta hanyoyi da dama, alum yana da muhimmanci sosai a rayuwar dan adam. Shiyasa a shekarun baya da wuya kaje gida ka tarar ba'a yin amfani da alum saboda ana yin magani dashi sosai. 


Mata a shekarun baya suna yin amfani da alum don yin maganin matsi, sai dai a yanzu ba kasafai ake yin amfani dashi ba a dalilin bayyanar wasu hanyoyi da ake yin amfani dasu don yin matsi. 


Hanyoyin Maganin matsi da alum

Hanyoyi 2 da ake yin amfani da alum don maganin matse gaban mace, gasu kamar haka 


1) Ana yin matsi da garin alum, za'a zuba kamar cokali 2 cikin cup is zuba ruwan dumi a juya sosai, za ki wanke gabanki da wannan ruwan garin alum, idan kinyi hakan sai ki samu ruwa mai tsafta ki wanke gabanki dashi. 


2) Za'a yi amfani da alum na dutse wanda ba gari ba, shi idan kin same shi zaki wanke shi don fitar da dukkan dattin dake jikinsa, za ki gogawa shi a gaban ki, iya gefen gabanki ake gogawa banda cikin farjin. Ki barshi yai kamar minti 30 sai ki wanke da ruwan dumi. 


Wannan sune hanyoyi 2 na yadda ake yin maganin matsi da alum, da fatan mata za su yi amfani da wannan hanyoyin kamar yadda muka bayyana. Sannan idan kun jarraba kunga ya muku aiki ku yi kokarin sanarwa da sauran mata. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post