Maganin dumin gaban mace |
Hanyoyin Yadda Ake Maganin dumin gaban mace
Su dai mata a kullum idan kaji suna neman magani bai wuce wanda za su yi amfani dashi don inganta zamantakewar su da mazajen aurensu. Hakan yasa yau na kawo muku yadda za ku yi don kara dumin gaba.
Maganin dumin gaban mace
Babu wani magani kai tsaye da yake jawo dumin gaban mace, sai dai akwai wasu abubuwa wanda idan mace tana yin su babu shakka gabanta zai dumi ya kasance koda yaushe cikin dumi. Ga abubuwan kamar haka;
1) yin tsarki da ruwan dumi koda yaushe, idan kina so ki kasance cikin damshin farji ki daina amfani da ruwan sanyi wajen yin tsarki. Ruwan dumi yana da matukar muhimmanci sosai ga mace.
2) sa pant akai akai amma banda dare. Ki daina zama babu pant a jikinki domin kuwa iska tana iya shiga wanda hakan kan iya haifar da matsala.
3) yawan hade kafan ki in kina zaune, ki ki guji bude kafafunki a lokacin da kike zaune ko a kwance, yi kokarin hade kafafunki a koda yaushe.
4) tsugunno kan rushi ko baki sa komai ba. Tsugunno kan masai na daga cikin abubuwan dake lalata dumin farji musamman masai irin na gargajiya.
5) lulluba da bedspread ne lokacin jima'i sai kuma nature. Akwai matan da su haka Allah ya halicce su basuda dumin farji.
Abubuwan Dake Rage Dumin Gaban Mace
1) ki yi kokarin daina yin amfani da tsarki da ruwa sanyi
2) yawan wawan zama, yi kokarin rufe cinyoyinki
3) rashin lulluba lokacin harka ko kuma fan ko ac na kunne,
4) saka yatsa a gaba, wasu matan suna saka yatsa a gaban su wannan na daga cikin abinda ke jawo rashin dumin gaba
5)a daina yawo ba tare da takalmi a tsakar gida
6) ko infection, cututtuka irin na infection na jawo rashin dumin gaban mace
Mata ku kiyaye sosai, idan kuna son dawwa mamammiyar ni'ima a jikinku, don ganin kun tsira da mutumcinku da kuma martabarku wajen mazajenku da kuma lafiyar al,aurar ku dole ne ku kiyaye abubuwan da za su haifar muku da mastala a rayuwar auren ku.