Maganin Daukewar Sha'awa |
Yadda Ake Maganin Daukewar Sha'awa
Game da matsalar daukewar sha'awa ko rashin sha'awa, akwai dalilai masu yawa dake haifar da hakan, sai dai zan taƙaita akan abubuwa uku kaɗai.
1 Sha'awa takan gushe daga jikin Mace ta dalilin wata cuta dake tare da ita, Misali kamar ciwon sanyi da sauran nau'o'in cutukan dake shafar ƴan uwa Mata a al'aurarsu.
2 Wani lokacin idan mace tana shan wasu ƙwayoyi masu ƙarfi na asibiti sukan gusar mata da sha'awa, Misali kamar magungunan hawan jini, ciwon Sugar, Sickler, Arthritis, Asthma, da sauransu.
3 Shafar Aljanu: Idan mace tana da matsalar shafar Aljanu(Musamman aljanun Soyayya) sukan ɗauke duk wata ni'ima daga jikinta kuma su haifar mata da daukewar sha'awa, ko jin zafi yayin saduwa, wata ma da zarar ta kammala Jima'i da maigidanta zata riƙa ganin Maniyyin yana zubewa, don haka ina mai bamu shawara kar muyi wasa da magani wajan kula da kanmu.
maganin daukewar sha'awa
Shawara anan ita ce idan kina fama da wasu daga dalilan nan dana lissafa na daukewar sha'awa, to lallai sai kin magance abun kafin kisha kowanne maganin don samun dawowar sha'awa din.
Sannan yana da kyau ki dinga cin abinci masu gina jiki da kara sha'awa, kamar su kwai, kankana, citta, tuffa, ayaba, lemon zaki da sauran kayan abinci hakan zai inganta lafiyar ku da kara muku sha'awa.