Maganin Daina Wasa Da Al'aura (Istimna'i)

Maganin Daina Wasa Da Al'aura (Istimna'i)
 Maganin Daina Wasa Da Al'aura (Istimna'i) 


Yadda ake Yin Maganin Daina Wasa Da Al'aura (Istimna'i) 


Sakonni sun yi yawa daga wajen masu bibiyarmu cewa suna son mu basu maganin rabuwa da istimna'i. Wasu suna cewa sun kasa dainawa domin abin ya gama bin jikinsu idan basu yi ba basa jindadi. 


A iya bincike na babu wani magani na istimna'i, amma dai akwai wasu hanyoyi da ake bi domin magance ko Kauracewa yin istimna'i. Ga su kamar haka;


1. Kaucewa kallon finafinan batsa, kallon fina-finan batsa na daga cikin abinda ke haddasa aikata istimna'i, yi kokarin goge dukkan wasu hotuna da video na batsa dake kan wayarku. 


2. Daina kallon hoton da tsiraici yai yawa ko ya bayyana a ciki, ballantana kuma hoton tsiraici. Domin Indai za ku kalli hoton tsiraici to dole sha'awa ta motsa idan kuma sha'awa ta motsa idan babu aure dole a yi istimna'i. 


3. Daina zama kai kadai akoda yaushe a cikin daki. Ka koyi zama cikin jama'a koda bakaso, ko zama a masallaci, kadaici cikin daki na taka muhimmiyar rawa wajen saka mutum yai tunanin aikata istimna'i. 


4. Kauracewa mu'amala da Mace wacce ba muharramarka ba, kai koda muharramarka ce yanzu abubuwan sun baci idan kanajin bazaka iya rike kanka ba... kai nesa da magana da ita.


5. Kauracewa zancen batsa yayin waya da wata ko wani. Kalaman batsa tsakani mace da namiji na daga cikin abinda ke tasiri wajen saka sha'awa wanda ke haifar da istimna'i. 


6. Rage yawan tunanin Mace ga Maza ko tunanin Namiji ga Mace muddin hakan na haifar da matsala


7. Tuba ga Allah tare da daukar Alkawarin rashin sake aikatawa har abada. Kuma ku kasance masu riko da addini hakan zai taimaka muku wajen daina tunanin aikata istimna'i. 


8. Bijirewa dukkan wani nau'in abu mai tayar Maka da sha'awa. Tare da tuna cewa gwargwadon tsananin son kai sabo idan ka kaurace masa gwargwadon kimarka agun Allah kenan


9. Rage yawan dakon finafinai a waya ko kallonsu a TV, wajibi ne ka kula da Kauracewa tura-turan finafinan da basu cancanta ba wanda idan ka kalla za kaji sha'awa tare dakai 


10. Jajircewa koda kaji idan baka yi shiba kamar zaka mutu ka daure karka aikata shi. Nemi lemon tsami ka jiqa kasha awasu sukan samu hakan ya karya musu sha'awa amma ba duk ba..


11. Jajircewa ga azumin Nafila musamman bin ayarin azumin Litinin da Alhamis. Wannan yana taimakawa sosai wajen rage tunanin sha'awa. 


12. Kaucewa karanta Novels da littattafai na batsa. Yi kokarin mayar da hankali wajen Karanta Alkur’ani maigirma. 


Wadannan sune hanyoyin bi domin Kauracewa dab'i auren sabulu, ko wasa da al’aura ko kuma istimna'i da Samari mata da maza ke yi a wannan lokacin. Da fatan za ku yi amfani da wannan hanyoyin da muka bayyana don Kauracewa yin hakan. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post