Lokacin Daukar Ciki Ga Mata - Android Pols

 

Lokacin Daukar Ciki Ga Mata - Android Pols
Lokacin Daukar Ciki Ga Mata

Lokacin Ciki Ga Mata/Juna Biyu Wato (Pregnancy Period Or Gestation) A Turance. 


JUNA BIYU:- Wani Irin yanayi ne da Mata ke kasancewa tsawon sati Arba'in (40 Weeks) Ana dawainiya saboda abinda ke cikin mace da Ita kanta me juna biyu din Kuma cikin ya kasu har zango uku first trimester, Second trimester da kuma third trimester Kuma kowa ne rukuni yana daukar kimanin Wata tara (9 months). 

Zaman mace da yunwa da rashin abinci mai gina jiki ne ke saka su shan wahala da dadewa suna nakuda.

Hakan ne ke Saka jinjirin dake cikin su ya Sha ruwan mahaifa watau (amniotic fluid) ta hanyar bakin sa da hancin sa.

Sanda wadannan ruwan mahaifa (amniotic fluid) ke shiga kwakwalwar yaro, to sai ya zamana kwakwalwar (brain) din sa sai ta cure (dunkulewa) guri daya.

Dunkulewar kwakwalwar yaro guri daya ne ke sa a a haifi yaro da daya daga cikin wasu gungun cutukan da ake kira "Neurological Diseases" watau cutukan kwakwalwa.

Dalilin da yasa kenan kuke ganin da zarar an haifi yaro a hannun midwives watau unguwar Zoma za ta yi ta dukan duwawun sa domin yayi kuka. Rashin kukan nasa shi ke nuna alamar yasha ruwan mahaifa. Shan ruwan mahaifa Kuma shike sa yaron ya ki yin Kuka.

Ta hakan ne za kuga lokacin da yaro zai fado Duniya baya iya kuka, idan ma ba ayi sa'a ba sai yazo babu rayuwa. Idan ma ya rayu sai ya zama kamar bai da hankali ko Kuma ya zama shekarun yaron da yawa baya iya ko zama balle wasu ayukka na mutane. Karshe sai ace aljannu ne na shafe shi.

Don haka akwai bukatar a dinga baiwa mata gero da abinci nai gina jiki, nama, kwae, wake, madara, yoghurt, da naman kaza musamman sanda suke dauke da juna 2 domin samun karfi yayin Nakuda.

Dafatan iyaye naza magidanta za'a Kula a irin wannan Lokaci. Allah ya horewa magidanta Abun dawainiya da kulawa dasu gwargwadon hali.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post