Lokacin Da mace tafi daukan ciki - Android Pols

Lokacin Da mace tafi daukan ciki

Lokacin Da mace tafi daukan ciki


Masana sun bayyana Lokacin Da mace tafi daukan ciki a likatance 


Yana da matukar kyau da kuma muhimmanci ace mace ta rike ranakun zuwan hailarta kamar dai yadda wasu likitoci suka yi bayani.

A wasu lokutan matsalar rashin haihuwa ga wadanda suka yi aure hakan ya na samo asali ne daga rashin fahimta akan al’amura da suka sha bamban, da kuma suka shafi yadda halin da jikin mace yake, wannan kuma har da Ovulation, wato lokacin da kwan haihuwar mace yake kyankyashewa. 

Ovulation shine wani lokaci da mace ke fafe kwan haihuwarta wanda da zaran ta fafe ta kusanci miji to shikenan, domin shine lokacin da mace tafi daukan ciki idan har an sadu da ita. 

Dukka duka 48hrs ne kachal idan ya wuce sai wani watan kuma, amma wasu lokutan bisa ga hikimar Allah kwan yakan kwana biyu yana jiran abokin tafiyarsa wato kwan namiji. akwai ciwon mara slightly painless contraction ba menses kikeyi ba menstral pains ne, ciwon daga hagu ko dama, wani lokaci idan kinji duka side biyu.

Lokacin ovulation lalle idan kina da kula zaki gane. Yakamata mu dinga kula domin akwai wani irin painless contraction da zakiji. Mun san fallopian tubes dinmu guda biyu hagu daya a dama. So duk wata daga gefe daya ne kwan zai fito.


Lokacin Da mace tafi daukan ciki

Ga kadan daga cikin alamomin ovulation: 

1- farko shine painless contraction zakiji wani irin ciwo a hagu ko dama.

2- zaki dinga jin menstrual pains slightly amma ba menses kikeyiba

3- Areola wato black point na nononki zai kara baki kuma nipple wato kan nononki zai mike yayi erect kuma akwai zafi kadan kadan musamman idan ana tabawa.

4- Vaginal fluid. Majina mai tsananin danko Wanda take zama kaman spring zai dinga fito miki a gabanki.

 5- Matsananciyar sha'awar namiji zai kama mace a wannan lokocin.

6- Temperature na jikin mace zai karu, jikin ta yana daukan zafi, kuma ba zazzabin rashin lafiya bane.

Lokacin ovulation ko kuma lokacin da mace tafi daukan ciki, wani lokaci ne na musamman da ya kamata mu kiyaye idan kuma mace ta yi rashin sa'ar maigida baya gari ko kuma ba kwanakin ta bane to lalle kinyi missing sai kuma wani watan.

Sai dai yana da matukar wahala gane wannan lokacin da mace tafi daukan ciki, musamman ga wacce take da irregula period.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

3 Comments

Previous Post Next Post