Amfanin shan bakin shayi, |
Amfanin shan bakin shayi ga lafiyar jikin dan adam
Ko kunsan shan bakin shayi na sa tsawon rai, binciken ya kara da cewa shan bakin shayi na hana tsufa da wuri ga masu shan sa.
Wasu kwararru a Hukumar Kula da gudanar da bincike akan cutar daji na kasa da kasa tare da babbar kwalejin London wato Imperial College sun gano muhimmanci da amfanin shan bakin shayi ke dashi a jikin dan adam.
Kwararrun sun kara da cewa ta'ammali da bakin shayi na sa tsawon rai sannan kuma yana sa kariya daga kamuwa daga sauran cutuka kamar haka;
Ciwon siga
Ciwon koda
Ciwon Hanta
Shanyewar barin jiki da hakarkari da kuma
Bayar da kariya daga kamuwa daga sauran cutuka na zuciya.
Sai dai kuma yawan shan shayi da madara na haifar da tashin zuciya, ciwon ciki da sauransu.
Shiyasa kwararru suka bayar da shawara shan bakin shayi don gudun kamuwa da wasu cututtuka.
Ina gayu masu jiki duk madara? Shin za ku iya komawa shan bakin shayi zalla ba tare da madara ba? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku a comment section.