Kina Samun Namiji Dake Da Wannan Halayen Kada Ki Bari Ya Kubuce Miki

Kina Samun Namiji Dake Damun Wannan Halayen Kada Ki Bari Ya Kubuce Miki
Kina Samun Namiji Dake Damun Wannan Halayen Kada Ki Bari Ya Kubuce Miki


Kina Haduwa Da Namiji Mai Irin Wadannan Halayen Rikeshi Gam Kin Samu Mijin Aure


Samun namijin kwarai mai Ilimi da tarbiyya a wannan zamanin abu ne mai matukar wahala. Amma abin mamaki wasu matan suna dace da samun irin wadannan mazan amma sai su yi musu rikon sakainar kashi har su Kubuce musu. 


Kaman yadda muka kawo muku wasu alamomi na dacen mijin aure kafin mace ta amince da mai sonta da aure, ga Karin wasu alamomin da suke tabbatar miki da kinyi dacen mijin aure:

 

1: Namijin daya damu da damuwarki; Duk namijin da kika fuskanci ya damu da ke babu shakka yana matukar kaunarki kuma yana son ki kasance mata a gareshi. 


2: Namijin da kullum sai ya kiraki ya tambayeki yadda kika kwana, kika wuni da kuma yi miki fatan tashi lafiya. A yanzu ba kasafai ake samun maza kulawa irin wannan ba sai kadan. 


3: Namijin Da Yake Baki Lokaci Baya fakewa da aiki yayi masa yawa, idan masoyan ki yana baki lokaci yadda ya kamata kuna soyayya kuma yana kulawa dake. 


4: Namijin da yake sauraronki yake baki hankalinsa a duk lokacin da kike son zantawa dashi na muhimmi.

 

5: Namijin da baya jira har sai kin tambayeshi, koda yaushe so yake ya fatan ta miki rai da wasu kyautuka na musamman. 


6: Namiji mai cika alkawari. Duk alkawarin da ya miki yana kokarin ya cika. Ba naki kadai ba har na wasu daban. Wannan ba mijin yadawa bane, rike shi gam.


7: Namiji mai furta miki kalaman so a fili, a baka da kuma kuna ku biyu. Ba kasafai ake samun mazan da suke bayyana kalaman soyayya ga masoyiya ba. 


8: Namiji mai kalamai masu kyau a lokacin farin ciki da kuma bacin ransa. Idan kina tare da namijin da iya kalaman masu kwantar da hankali da huce bacin rai ki rike shi da kyau. 


9: Namijin da yake da zumudin bashi dama yaga iyayenki ko magabatanki. Duk namijin da baya miki zancen aure ko kuma idan kikai masa yake basarwa ki rabu dashi. 


10: Namiji mai nuna miki farin cikinsa da kuma yi miki godiya a duk lokacinda kika yi abun a yaba miki. Da kallon kwalliyarki ya yaba. Idan kin kawo masa ruwa ko abinci ya jisu daban da wadanda ya saba.


11: Namiji mai amafni da wadannan kalmomin guda biyu, magiya idan zai saki masa wani abun. Ya kuma ce ya gode idan kika masa, (please and thank you).


12: Namijin da baya kunyar a ganki da shi. Idan ba dagaske yake Sonki ba bazai so a dinga ganinku tare ba. 


Wannan sune abubuwan ko kuma halayen irin Namijin da mata za su rike, idan kika samu namijin dake da wadannan abubuwan da muka lissafa kiyi kokarin rike shi da kyau domin kin samu mijin aure. Da fatan mata zasu kula da wadannan abubuwan ba su maida hankali akan aljihunsa ko abun hawansa ba.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post