Ka Guji Yin Wadannan Dabi'un Ga Matar Da Zaka Aura

Ka Guji Yin Wadannan Dabi'un Ga Matar Da Zaka Aura
Ka Guji Yin Wadannan Dabi'un Ga Matar Da Zaka Aura 


Kada ka sabawa macen da zaka aura da wadannan halayen 


Akwai abubuwan da wasu mazan ke yiwa 'yan matan da za su aura wanda kuma daga baya suke yin nadama, hakan yasa na shirya kawo muku wasu dabi'u da za ku Kauracewa yi da macen da kuke soyayya da ita. 


1 kiran ta ko kuma yi mata sakon text a kullum, Kada ka Takura da yin kira a kullum. Ba wai an ce Kada ka dinga kiranta ba, aa ba ana nufin koda yaushe 


2 Kada ka ce za ka yiwa mata duk abinda take bukata domin hakan zai iya baka matsala bayan kun yi aure. 


3 Rashin Nuna mata Kuskuren ta, idan macen da kakeso baka nuna mata abubuwan da take yi ba daidai bane za ka yi nadama daga baya. 


4 macen da ake son a aura ba'a nuna mata ko kuma saba mata da akwai, ma'ana koda yaushe ka nuna mata kai mai shine. 


5 Yi mata karya saboda faranta ma ta, babu abinda yafi zubar da kimar namiji wajen mace musamman idan ta fuskanci kana yi mata karya. 


6 Daukar nauyin bukatun ta da su kafi karfin ka, Kada ka dauki nauyin bukatar matar da kake son aure domin ita ba ta zama matarka ba tunda ba'a daura muku aure ba 


7 Tabbatar ma ta da ita kadai ce bayan auren ku, Kada ka nunawa mace cewa ita kadai ce macen da za ka iya rayuwa da ita 


8 Ba ta Muhimmanci fiye da komai, Kada ka Nunawa macen da Zaka aura tafi komai muhimmanci a gareka. 


9 Cin mutuncin wasu a gabanta saboda ita, Kada ka yi kokarin cin zarafin wasu kawai don ka birge matar da kakeso 


Saba ma ta da abinda kasan ba zai dore ba, idan kasan baka da halin yin wannan abin Kada ka saba ma ta dashi 


Wannan sune abubuwan ko halayen da maza za su kiyaye Kada su sabawa macen da zasu aura. Domin su mata kwakwalen yara ne dasu, duk abinda ka dora mace akai to fa haka za ta dore.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post