Irin Namijin Da Mata Basa Iya Mantawa Dashi Duk Tsawon Zamani

Irin Namijin Da Mata Basa Iya Mantawa Dashi Duk Tsawon Zamani
Irin Namijin Da Mata Basa Iya Mantawa Dashi Duk Tsawon Zamani 


Irin namijin da zaiyi wasa da ita, ya tattauna da ita, ya shiga lamuranta sosai da sosai.


Wanda ya iya sauraro, zai saurari zancen ta kuma yana maraba da shi na daidai da rashin daidai, cikin kulawa da biye mata, baya kushe ta ko gwale ta.

Namiji wanda baya wasa da abin da ya shafe ta mai dadi ko mara dadi sai inda karfinsa ya kare.

Namiji mai juriya da Hakuri da ita sosai kan daidai da rashin daidai dinta, mai yi mata fada da nasiha cikin kulawa.

Mai yawan kyauta, me fara'a me iya bayar da kulawa, kamar yi mata tausa idan mijinta ne lokacin da ta gaji, yi mata sannu da zuwa idan ta dawo daga unguwa da tambayar ta hanya, kiranta idan tayi tafiya yaji yaya ta sauka ko ya ta kwana? Idan tayi wasu kwanaki zata dawo har yayi mata girki idan yana gida ko ya ajiye wani abu domin ta, wanda baya son ya bata mata Rai da ganganci yana kula da motsinta sosai na farinciki ko damuwa, yayi iya yinsa wurin ganin tayi nishadi idan damuwa ce.

Irin namijin da zaiyi wasa da ita, ya tattauna da ita, ya shiga lamuranta sosai da sosai.

Wanda ko yaushe yake son cigabanta da ganin Burinta me kyau ya cika indai yana da yanda zaiyi.

Mai girmama komai nata da kowa nata, me girmama ta da daraja ta, da tsayuwa kan tsare mutuncinta.

Wannan sune halayen namijin da mata basa iya mantawa dashi, duk macen da ta rayu da irin wannan namijin da wuya ta kara jin dadin rayuwa da wani a duniya, wasu sun samu namiji mai irin wannan halin amma kuma suna wasa da irinsa, wasu basu samu ba suna neman irinsa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post