Irin Macen da maza suke Nadama idan suka rasa ta

Irin Macen da maza suke Nadama idan suka rasa ta
Irin Macen da maza suke Nadama idan suka rasa ta


Irin Macen da maza suke Nadama idan suka rasa ta: Mace me gaggawar yin abin da miji yake so, da gudun abin da baya so da dukkan kokarinta


Akwai wasu nau'in mata wanda idan namiji ya same su yana fargarbar rasa su da kuma nadama idan sun rabu. Irin wannan matan suna da wuyar samu musamman a wannan lokacin da muke ciki na sauyawar zamani. 

Duk namijin da yake da mace mai irin wannan halayen yana shiga firgici da yin nadama a duk lokacin da ya rasata. Ga irin halayen Matan kamar haka. 

Mace me taya su biyayyar Iyaye da kyautata musu, me nusar da su kan sadar da zumunci.

Macen da bata masa karya kuma bata jawo masa magana, kuma ko rantsuwa yayi kanta kan shaidar kirki bashi da kaffara.

Macen da abin Hannun miji bai tsone mata Ido ba kawai shi yake gabanta, ko miliyan 100 zai irga a gabanta abin da ya ďauka ya bata shi take karba tayi godiya ta sa Albarka.

Mace me gaggawar yin abin da yake so, da gudun abin da baya so da dukkan kokarinta.

Macen da duk girman sabani bata fasa yi masa duk abin da ta saba masa, girki, gaisuwa, zuwa shimfida da kamshi, da sauransu ko da ranta a bace yake.

Mace me bashi hakuri, me godiya kan me yawa da kadan, me tattali da Adana komai na shi, me tsananin tausayin sa akan komai.

Macen da bata so ya wuni a Gida ko ya dawo bai ga Adonta ba ko jin kamshinta, me kula da motsin sa na damuwa da farinciki ta bishi da Lallashi.

Mai Ibadah, da karatun Qur'ani da Ambaton Allah, me son a Bautawa Allah kuma ayi masa biyayya, me gudun Haram me son a kyautata.

Macen da yana kyautata mata tana gode masa, ko ita ta kyautata masa ya gode zata kara gode masa akan ya gode mata, idan ya wadata ta da Abinci da bukatu za ta gode tayi Addu'a, idan ta faranta masa zata gode da yayi farinciki da abin da tayi masa.

Mace me tsananin son zaman lafiya da kowa, da son ayi wa kowa Adalci, bata son kanta akan Abokan zama, tafi son kowa ya samu kwanciyar Hankali, me bayar da kyakkyawar Tarbiyya ga danta ko ga duk wanda aka bata Amana.

Wasu sun samu amma basu san tsadar ta ba itace ma tafi kowa shan wuya a hannun su, sai sun rasa sai su zo sufi kowa Kuka, wasu kuwa kallonta suke kamar kowacce kala suka dakko hakan take, wasu kuma nemanta suke da dukkan abin da suka mallaka ma amma basu samu ba. Allah ya zaba Alkhair. Ameen.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post