Illar Auren Sha'awa Da Samari Ke Yi A Wannan Zamanin |
Annabi (SAW) Ya bada muhimmanci a auri mace saboda addininta da kyawawan halayenta
Auren sha'awa rashin sani ne, Wadanda basu san sirrin zaman aure ba wato samari, gani suke zaman aure shine ayi jima'i a ji dadi, lallai ba haka abin yake ba a zaman aure.
Da zaran an daura auren saurayi da budurwa, ana kashe wutar sha'awa a watanni uku bayan aure, wato daga lokacin da ta fara dawainiyar daukar ciki, daga nan har zuwa lokacin da zaku koma ga Allah hakuri ne zai biyo bayan zaman aure.
Shiyasa Annabi (SAW) Ya bada muhimmanci a auri mace saboda addininta da kyawawan halayenta, idan ance mutum yana da addini to ya kunshi har kyawawan halaye.
Zaku iya ganin Musulmi ya tara ilmin addini sosai har ya zama Malami amma bashi da addini, ma'ana bashi da kyawawan halaye.
Kyawun fuska da kalar fatan jiki da diri wannan abune da yake burge kwayar idanu kadai, mata duka halittarsu daya ne, abinda zaka ji a jikin mace mai kyau haka zakaji a jikin wacce bata da kyau, ba zaka zaka gane matsalar mace mai kyau marar addini ba sai bayan ka aureta.
Saboda haka bayin Allah samari ku yi kokarin auren mata masu addini amma sai kun zama masu addini tukunna, kar ku bari kyawun sura ya yaudareku daga baya kuzo kuna da na sani marar amfani.