Hanyoyin warware sihiri a musulunci |
Hanyoyin Yadda Ake warware sihiri a musulunci
Yau insha Allah zan kawo muku bayanai a takaice kan hanyoyin da za'a yi amfani dasu don warware sihiri kamar yadda addinin musulunci ya bayyana.
Kamar yadda aka sani warware sihiri ba abune mai sauki ba, kuma kowa yasan cewa sihiri zai iya yin tasiri a kansa, don haka babu wani mutumin da zai cewa yafi karfin sihiri domin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW shima an yi masa sihiri kima ya yi aiki a kansa.
Hakan yasa za mu yi muku wasu takaitaccen bayani kan yadda za ku warware sihiri da Kanku idan hakan ya faru daku. Sannan kuma za ku iya taimakawa wanda yake fama da sihiri don magance masa.
Hanyoyin warware sihiri a musulunci
A cikin wannan darasi na yau hanyoyi 3 ne da za ku iya yin amfani dasu domin ku warware sihiri. Ga su kamar haka;
1. Za a samo ganyan magarya guda 7 a dan dakasu da dutse sai azuba a ruwa, sannan sai a kawo ruwan kusa da baki Ayi bismillah a karanta wadannan ayoyin na Alqurani kamar haka;
1. Suratul fatiha
2. Kursiyyu
3. Suratul kafirun
4. Suratul iklas
5. Suratul falaki
6. Suratul nas
Acikin suratul a'araf aya ta 117 zuwa ayata 122, A suratul yunus aya ta 79 zuwa ta 82, A suratu daha aya ta 65 zuwa 69.
Za asha ruwan yadda iskan bakin maikaratu zai dinga kada ruwan. Bayan angama sai a zuba wanda za asha, sauran kuma sai ayi wanka akan tawul ko a baho. Idan angama a zuba a inda babu najasa, haka za ai kaman kawna 3 za'a sama lafiya in sha Allah.
2) Sannan kuma idan har baka Iya karatu ba Zaka je Islamic chemist ka nemi a baka wadannan abubuwan kamar haka;
Bakurul sihir hayaki ne
2. Abaka ilajussihir na ruwa
3. Abaka almujarrab na baslin
4. Abaka shayin shai danu
Ko wanne magani sun rubuta yadda ake anfani dashi ajikin kwalin, itama wanna hanya ce ta warware sihiri.
3. Ana warware cutar aljani da sihiri da Habbatussauda, a hadata da zuma da man zaitun anasha, Gami da junnu kuwa ana samun Hiltit Warinsa yana shake aljani har ya halakashi, ana hadiyarsa Kadan kadan insha Allah
Albabunaj
Anayin shayinsa asha yana Maganin duk wata cuta da aljani yasata, amma sharadin, Idan ansha a yawaita shan ruwa.
A takai ce wannan sune hanyoyin warware sihiri a musulunci, da fatan Allah ya bada lafiya, kuma Allah ya tsare mu da kamun sihiri ko wane iri ne amin.